
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
An buƙaci gwamnatin jihar Katsina da ta raba tirela 20 na shinkafar da gwamnatin tarayya ta bayar a watan da ya gabata domin rage raɗaɗin yunwa da hauhawar farashin kayan abinci.
Wani shugaban al’umma, Alhaji Ɗayyabu Gwajo ya faɗi haka a wata ziyara da ya kai cibiyar ƴan jarida sashin kafofin yaɗa labarai a Katsina.
Ya ce, ya na sane da kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa na tsara yadda za a raba shinkafar sai dai kamar yadda ya faɗawa manema labarai, kwamitin ya ɗau tsawon lokaci.
“Kwamitin ya ɗauki tsawon lokaci. Har yanzu bai bada rahotonsa ba. Ga mutane na fama da yunwa” inji Gwajo.
Har’ila yau, ya ƙara da cewa, kwamitin na iya samun adadin mutane mabuƙata da masu lalurar da za a ba su shinkafar a ƙananan hukumomin jihar.
Haka ma, ma’aikatan cikin gida na tsaro na iya samu da ƴan gudun hijira a faɗin jihar waɗanda zasu amfana da shinkafar.
A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta bai wa kowace jiha tirela 20 na shinkafa domin raba wa al’umma domin rage raɗaɗin tsadar rayuwa gare su.
