Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wani iftila’i ya afku a ƙauyen Runjin Barmo da ke gundumar Kajiji a ƙaramar Hukumar Shagari a Jihar Sakkwato, yayin da wasu mutum bakwai ‘yan gida ɗaya suka mutu bayan sun ci wani gurɓataccen abinci na rogo.
An tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da Nura Bello, jami’in yaɗa labarai na ma’aikatar lafiya ta jihar Sokoto, ya fitar a madadin kwamishinar lafiya ta jihar, Hajiya Asabe Balarabe, a yammacin Lahadi.
A cewar sanarwar, hakimin ƙauyen, Malam Muhammadu Modi, ya bayyana wa kwamishinan abubuwan da suka faru a lokacin da ta jagoranci wata tawaga zuwa ga yankin da abin ya shafa.
Iyalan da suka rasu sun haɗa da Malam Abubakar, da matarsa A’ishatu Abubakar, da ‘ya’yansu biyar.
Iyalan sun ci rogon da ake zargin gurɓataccen rogo ne a lokacin da suke cin abinci a ranar Larabar da ta gabata.
“Har yanzu ba a tabbatar da ainihin musabbabin mutuwar,” inji Malam Muhammadu Modi.
Ya kuma ƙara da cewa, wasu gidaje huɗu ne sun yi amfani da irin wannan rogo a ƙauyen, inda babu ɗaya daga cikinsu da ya ba da rahoton wani abu na daban, lamarin da ya haifar da damuwa da kuma tambayar takamammen musabbabin faruwar lamarin.
Hakimin ƙauyen ya miƙa godiyarsa a madadin al’umma ga Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, bisa gaggauta ɗaukar mataki da kuma nuna damuwarsa kan wannan mummunan lamari.
A yayin ziyarar, kwamishiniyar Hajiya Asabe Balarabe ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga al’ummar da suka rasa rayukansu.
Ta kuma ba su tabbacin cewa gwamnatin jihar na ɗaukar lamarin da muhimmanci kuma za ta gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwar.
Ma’aikatar tana shirin tattara samfurori daga matashin da ya shuka rogon, wanda zai iya ba da muhimman bayanai game da musabbabin faruwar lamarin.
Kwamishinar ta kuma buƙaci mazauna jihar da su sanya ido tare da gaggauta kai rahoton duk wani abin da ba a saba gani ba a fannin kiwon lafiya ga ma’aikatar lafiya.
Ana sa ran gwamnatin jihar Sakkwato ta ma’aikatar lafiya ta jihar za ta ɗauki matakan da suka dace bisa ga sakamakon binciken da ake yi, domin tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba.
