Gwamna Dikko Raɗɗa na Katsina ya dawo bakin aiki

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya dawo bakin aikinsa bayan shafe wata guda ya na hutu.

Bayan kammala hutun a makon jiya sai ya wuce ƙasar Sin tare da manyan jami’an gwamnatinsa domin neman masu zuba hannun-jari akan harkar noma da ƙere ƙere.

A lokacin da ya ke ganawa da manema labarai bayan dawowarsa daga Sin, gwamnan ya ce ya yi tafiyar ne don ya huta da kuma duba lafiyarsa.

Malam Dikko Raɗɗa ya godewa al’ummar jihar Katsina a bisa juriya da haƙuri da suka nuna a lokacin da baya nan .

Ya kuma jinjina masu bisa haƙuri da suka nuna a lokacin da aka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa.

Gwamna ya bayyana cewa, ya na sane da halin ƙunci da al’ummar jihar ke ciki inda ya tabbatar masu da ce gwamnatin ba zata gajiya ba wajen samar da hanyoyin warware matsalolin rayuwa.

Bugu da ƙari, ya bayyana wasu matakai da gwamnatinsa ta ɗauka na inganta rayuwar al’ummar jihar waɗanda suka haɗa da tallafawa masu ƙananan sana’o’i da samar da aikin yi da gina hanyoyi da sauran su.

“Da yardar Allah za mu cigaba da aiki tuƙuri na taɓbatar da adalci da kuma samar da ababen more rayu”, inji shi.

Ya kuma gode wa Mataimakinsa, Faruk Lawal Joɓe bisa yadda ya riƙe jihar da amana da ƙoƙarin da yayi na kawo sauƙi ga al’ummar jihar.

Ɗaruruwan mutane ne suka yi dafifi a filin jiragen sama na Umaru Musa Yar’adua a Katsina waɗanda daga ciki akwai kakakin Majalisar Dokoki da sarakunan Katsina da Daura.

By Babaji