
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga sarkin Ingila, Sarki Charles na uku a Fadar Bakinham da ke birnin Landan don gudanar da ganawa ta kai-da-kai a wani mataki da ke nuni da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Najeriya da ƙasar Ingila.
A rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samo, wannan ita ce ganawa ta farko tsakanin shugabannin biyu tun bayan haɗuwarsu a wajen taron canjin yanayi karo na 28 da aka yi a bara a ƙasar Dubai. Ganawar ta yanzu ta biyo bayan amsa gayyatar da sarkin na Ingila ya yi ma sa.
Shugabannin sun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi ƙasashen Duniya, tare da mayar da hankali kan ƙalubalen canjin yanayi da ake fuskanta.
Shugaba Tinubu da Sarki Charles sun kuma yi amfani da damar domin yin haɗin-gwiwa game da halartar taron canjin yanayi karo na 29 da ke tafe wanda za a gudanar a Azerbaijan, da kuma taron ƙasashe renon Ingila da za a gudanar a Samoa.
Shugaba Tinubu ya bayyana ƙoƙarin da Najeriya ta ke yi wajen magance matsalar canjin yanayi tare da bada tabbacin cigaba da bin tsare-tsaren Duniya domin samun ci gaba mai ɗorewa.
