Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwamnatin Nijeriya ta musanta raɗe-raɗin cewa ta ƙara yawan harijin kayayyaki na ‘ɓAT’ zuwa kashi 10%, daga kashi 7.5%.
Ministan Kuɗi na Nijeriya, Wale Edun a cikin wata sanarwa ya ce har yanzu dokokin ƙasar sun ƙayyade cewa hariji kayayyakin da ake biya kashi 7.5% ne.
Ya ce: “Harajin kayayyaki a Nijeriya yana nan a kashi 7.5% , kuma hakan gwamnati ke karɓa. Domin haka gwamnati da dukkan hukumomin ta suna biyayya ga wannan tanadi na doka, kuma ba za su saɓa ba.
Rahotan da aka riƙa yaɗawa game da ƙarin harajin kayyakin a Nijeriya ya janyo martani daga ɓangarori da dama, ciki harda na ’yan siyasa.
Tuni dai tsohon mataimakin shugaban ƙasar kuma ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da matakin.
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sada zumuntansa na ɗ.
Ya bayyana matakin a matsayin wani abu da zai yi mummunar illa ga al’ummar Nijeriya, yana mai hasashen cewa hakan zai kara ta’azzara matsalar tsadar rayuwa da ƙasar ke fama da ita da kuma kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.
“ƙara kuɗin haraji zai zama wuta mai zafi da za ta cinye ainihin mutanenmu,” inji Atiku.
“Wannan matakin zai haifar da koma baya da ƙara zurfafa matsalar tsadar rayuwa a cikin gida da kuma ƙara tabarbarewar ci gaban tattalin arzikin ƙasar ne kawai”
