Tinubu ya jajenta wa mutanen da hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu ya jajenta wa gwamnatin Zamfara kan ambaliyar wasu sassan jihar da kuma mutanen da hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 40 a ƙaramar hukumar Gummi.

Ya bayyana alhininsa kan musibun da suka samu mutanen yankin da ma jihar baki ɗaya tare da yin alƙawarin tallafa wa mutanen da lamarin ya shafa.

Shugaba Tinubu, ya kuma umarci hukumomin bada agaji su yi nazari game da dalilan faruwar abubuwan biyu don gano haƙiƙanin matsalolin da suka haddasa hakan.

Ya kuma umarce su da su yi aiki da gwamnatin jihar wajen taimaka wa mutanen da annobar ta shafa.

By Babaji