
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jajenta wa gwamnatin Jihar Borno da mutanenta biyo bayan ambaliyar ruwan sama da aka yi a Maiduguri, babban birnin Borno.
Gwamna Lawal, wanda Sakataren gwamnatinsa, Malam Abubakar Nakwada ya wakiltce shi, ya jagoranci tawagar gwamnatin Zamfara zuwa gaisuwar jajen a ranar Alhamis.
Kakakin gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya ce dalilin ziyarar shi ne don a jajenta wa gwamnatin Borno da mutanen jihar kan ambaliyar wacce ta auku a makon da ya gabata, kamar yadda ya faɗa a cikin wani saƙo da ya fitar.
A lokacin da ya ke gabatar da jawabi yayin ziyarar Malam Nakwada ya sanar da cewa, gwamnatin Zamfara ta bada tallafin Naira miliyan 100 ga Borno don a raba wa mutanen da lamarin ya rutsa da su da kuma ƙarfafa alaƙar taimakon juna a tsakanin gwamnatocin biyu.
Ya kuma bayyana takaici ganin yadda ambaliyar ta raba sama da mutane miliyan ɗaya da matsugunansu, ya na mai fatan kar irin hakan ya sake faruwa a nan gaba.
