PDP ta zargi gwamnatin Kebbi da yawon sharholiya 

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Jam’iyyar PDP ta adawa a jihar Kebbi ta nuna rashin gamsuwa bisa ga yawace-yawacen da ta ce Gwamna Malam Nasir Idris ƙauran Gwandu yana yi ba tare da dawowa da wani sakamako mai amfanin al’umma ba.

Wannan yana ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannun Sakataren Jam’iyyar Honarabul Abubakar Bawa Kalgo da aka raba wa manema labarai ranar Lahadi 15 ga wannan watan na Satumba 2024.

Takardar ta ayyana cewa tun bayan da aka rantsar da Malam Nasir Idris a matsayin gwamna a jihar sama da shekara ɗaya kenan ya rinƙa ɗibar ‘yan uwa da abokan arziki zuwa yawon gantali a ƙasashen ƙetare da sunan neman abokan hulɗa don kafa jari a jihar amma har yanzu babu wani takamaiman abin a zo a gani da wannan yawon ya haifar sai dai kawo nakasu ga asusun jihar wanda PDP ba za ta zura ido tana kallo ba.

Takardar ta bayyana cewa a maimakon haka ya kamata ya tsaya gida ya sa idon basira ya samar da abubuwan cigaba da suka haɗa da bunƙasa noma ƙanana da matsakaita zuwa manyan masa’antu, ƙirƙiro sana’o’i da kuma bayar da tallafi daban-daban ga matasa da mata da dai sauransu saboda jihar Kebbi kowa ya sani jihar ce da Allah albarkace ta albarkatun ƙasa daban-daban, wanda yin haka ya fi wannan yawon ana ta watanda da dukiyar al’umma ba tare da wani sakamako ba.

A ɗaya ɓangaren ita ma jam’iyyar APC ta mayar da martani inda Sakataren yaɗa labarai na Jam’iyyar Malam Isah Abubakar Assalafi ya bayyana wa wakilinmu da cewa “wannan mulki ne na dimukuraɗiyya wanda ya bai wa kowa ‘yancin fadar albarkacin bakinsa saboda haka ba za a  hanawa kowa faɗa ba amma dai duk wanda ya bar jihar Kebbi shekaru biyu idan ya dawo yau ba ƙaramin mamaki zai yi ba bisa ga irin cigaban da aka samu.

“Wannan ana neman yaudarar al’umma ne ta hanyar karkatar da tunanin su ta hanyar bai wa wannan gwamnati suna amma duk wanda ya sa abinda ya ke yi ya san wannan gwamnati tana da tsare-tsare da ta ke yi don inganta rayuwar ‘yan jihar ta fannoni daban-daban.

“Waɗannan tafiye-tafiye da maigirma gwamna ke yi mu mun san ya haifar da ɗa mai ido, saboda idan muka duba a ɓangarorin ilmi, noma, da kuma uwa uba fannin kiwon lafiya, wanda bai sani ba dai shi ne bai sani ba.

“Kuma yanzu haka gwamna Nasir Idris ya buɗe ƙofofi daga kamfanonin ƙasashen ƙetare don shigowa su kafa kasuwanci a jihar saboda amfanin al’umma ta fannoni daban-daban,” inji shi.

Haka-zalika Malam Isah Abubakar Assalafi ya yi kira ga jam’iyyar adawa ta PDP da ta daina sakin maganganun da ba su da madogara a maimakon haka su rinƙa yin tunanin abubuwan da za su kawo cigaba a jihar.

By ukarofi