Ƙungiyar ARTPAN ta zaɓi Alhaji Haruna Mohammed a matsayin sabon shugabanta

Spread the love

Daga DAUDA USMAN

Ƙungiyar Sufiri ta ARTPAN a Nijeriya, ta amince da zaɓar tsohon shugaban kasuwar Mile12 da ke cikin birnin Legas, Alhaji Haruna Mohammed a matsayin sabon shugabanta na ƙasa gabaɗaya.

Shugabannin ƙungiyar na ƙasa da kuma wakilanta na jihohi 36 har da Babban Birnin Tarayya Abuja su ne suka tabbatar da hakan a lokacin gudanar da taron ƙungiyar a Abuja.

Taron bikin amincewa da zaɓar sabon shugaban ƙungiyar na ƙasa ya samu halartar dukkan shugaban nin ƙungiyar na ƙasa da sauran wakilan ƙungiyar na jihohi 36 da kuma masu ruwa da tsaki a ƙungiyar.

Bayan kammala taron ƙudirin zaɓar Alhaji Haruna Mohammed a wannan matsayi, shugabannin sun miƙe suka bayyana amincewarsu na zaɓar Alhaji Haruna Mohammed a matsayin sabon shugaban ƙungiyar na ƙasa.

An rantsar da shi a wannan matsayi tare da miƙa masa takardar shaida da kuma kundin tsarin mulkin ƙungiyar gabaɗaya.

Sabon shugaban ƙungiyar ya gabatar da jawabansa na godiya tare da nuna amincewar sa a game da zaɓen da aka yi masa, sannan ya cigaba da gabatar da saƙonsa na godiya ga shugabannin ƙungiyar na ƙasa da sauran wakilanta na jihohi Nijeriya bakiɗaya.

Haka zalika, sabon shugaban ya ce yana isar da saƙon sa na godiya ga dukkan shugabannin ƙungiyar na ƙasa da wakilanta na jihohi da sauran mambobin da suka ga ya cancanta suka ba shi wannan matsayi.

Ya ce, yana fatan Allah Ubangiji ya saka wa kowa da alheri, sannan ya roƙi Allah Ubangiji ya shige masa gaba a wajen jagorancin ƙungiyar, kuma ya ba shi ikon riƙe ƙungiya hannu bibiyu.

Sabon shugaban ƙungiyar ta ARTPAN ya yi amfani da wannan damar ya nuna rashin jin daɗinsa a game da abubuwa da suka faru a waɗansu jihohi na arewacin Nijeriya ta sanadiyyar zanga-zangar lumana.

Ya ce, da fatan matasa masu irin waɗannan miyagun halaye za su kaucewa aikata hakan a nan gaba.

By ukarofi