Amharawa: Masu tarbiyyantar da ’ya’yansu ta hanyar dabbobi

Spread the love

‘Yan ƙabilar Amhara waɗanda aka fi sani da Abyssinians, ƙabilu ne da ke a Arewa da Tsakiyar tsibirin ƙasar Habasha. A bisa wata ƙididdiga da aka gudanar ta ƙasa, a shekarar 2007, jimillarsu ta kai yawan sha tara zuwa ɗari takwas da bakwai da kuma ɗari takwas da sha bakwai, inda suka haɗa da, kashi ashirin da bakwai da digo sha biyu na yawan al’ummar.

Waɗannan al’umma, ana kuma sa su a cikin jerin kwararrun ’yan ƙasar ta Habasha da ke Arewacin ƙasar Amurka. Al’ummar, suna ikirarin su jinsin Sarki Solomon ne kuma su mabiya addinin Kiristanci ne. Suna magana ne da yaren Nahiyar Asiya da kuma maganar zaurance ta Habasha.

Al’umar Amhara, suna amfani ne da suturarsu ta al’ada da suke sanyawa mai ɗauke da farin gashi da yafa tawul da kuma bargo marar nauyi a ƙafadunsu. Mafi yawancinsu suna zaune a tsibirai a matsayin rigakafin wani tirniƙi da zai iya faɗa musu, sai dai, hakan yana haifar masu matsalar yin tafiye-tafiye da kuma samun wasu ababen da suke buƙata na rayuwa.

Mazajensu, suna zama ne a fili matan su kuwa ɗaura da gidajen mazajen nasu, ’ya’yansu kuma a cikin gida suna kula da dabbobi. Su kananan manoma ne, suna yin noman ne ta hanyar sanya wani sanadari da suke sanyawa a kan irinsu in za su yi shuka, idan shukar ta kai lokacin girbi, suna yi ne da hannayensu.

Suna yin girki ne da kashin dabbobi da suka shanya a gona bayan sun bushe. Abicin da suke ci ana kiran sa Injera bo wot wanda ake sarrafa shi da wani hatsi na gida, sai dai ga mutanen Habasha, irin abincin, ba cimar su ba ce. Akan kuma haɗa abincin da wake da nama. Yadda ake sarrafa abincin akwai cin rai matuƙa da kuma cin lokaci ga masu sarrafa shi. Rashin tsaftaccen ruwan sha da rashin shuke-shuke, suna ɗaya daga cikin ababen da suka addabi al’ummar.

Bugu da ƙari, irin waɗannan matsalolin da ire-irensu, sukan jefa al’umar a cikin matsalar ƙaracin abinci a tsibiran nasu. Irin wannan annobar ta yunwa ta taɓa addabar al’ummar a shekarar 1974 da kuma 1984. ’Ya’yansu masu shekaru biyar zuwa shida, sukan shafe lokutansu ne wajen lura da dabbobi da tumakan iyayen su.

Wani abin sha’awa shi ne, yadda yaran suke halartar makarantun gwamnati, sai dai suna zuwa darasin ne na rabin rana saboda ɗimbin ɗaliban da ke halartar makarantun. Kimanin kashi goma bisa ɗari ne na al’ummar suke da hanyar wucewa, kuma suna zama ne a cikin matsananciyar rayuwa.

’Yan ƙabilar ta Amhara mutane ne da suke takama da kansu da ƙabilarsu da addininsu a faɗin Duniya. Sun ƙarfafa al’adarsu a ƙarni da dama da suka shige, kuma ba su yarda wasu sababbin al’adun duniya sun gurbata musu al’adu ko addininsu ba.

Matsugunansu, sun gina su ne a kan tsaunuka don kariya daga ambaliyar ruwa, haka gonakinsu, a kan tsaunuka suke don kauce wa zai-zayar ƙasa. Dakunan kwanan ’ya’yansu maza na kusa da dakunan iyayensu maza, kuma suna aurar da ‘ya’yansu mata suna da shekaru sha huɗu, inda angwayen amaren sukan dara su da shekaru uku ko shekaru biyar. Sai dai, wannan al’adar ta auren, ta tsaya ne kawai a karni na ashirin. Kodayake, gwamnatin mulkin mallaka ta ƙasar, daga baya ta tilasta sai yarinya ta kai minzalin shekaru sha takwas za a iya aurar da ita.

Mafi yawancin auratayyar ana gudanarwa ne ta hanyar tattaunawa tsakanin iyayen ango da na amarya ta hanyar gudanar da shagulgula don ƙulla igiyar aure. A ƙa’idar ɗaura auren, ba lallai ba ne sai inda limami mai ɗaura aure, haka kuma an bada damar a yi saki, tare da yin yarjejeniya kafin a wanzar da shi.

Al’ummar sun yi amannar ƙulla auren wucin-gadi ta hanyar sanarwa da baki a gaban shaidu, inda amarya za ta bada sadaki ga mai mata hidima a gida, sai dai, ba maganar gado tsakanin angon da amaryar, amma ’ya’yan da suka haifa, za su iya cin gadon iyayen nasu. Malamansu ns addini kan yi aure idan sun so sai dai, ba za su iya yin saki ba, idan an samu haihuwa a auren, malaman na su za su je dangin matar tasu su yi wa abin da aka Haifa addu’a.

Abin da aka haifa da mai jegon, za su zauna a gidansu mai jegon har tsawon kwana arba’in don ita da abin da aka haifa, su samu ƙarfin jikinsu. In namiji aka haifa bayan kwana arba’in, za a kai shi Coci don a yi ma sa Baftisima, in mace ce kuwa, bayan kwana tamanin da haihuwa. Ma su jego suna shayar da ’ya’yansu har tsawn shekara biyu, ana bai wa yara ladabi har zuwa shekaru biyar zuwa bakwai, inda daga baya, in sun balaga za su iya yin sharholiyarsu amma a bisa ladabin da aka ba su.

A bisa tatsuniyoyin nasu, abin bautarsu yakan yi wa mace baki ko ɗibar jininta duk wata domin a tunatar da ita cewa wata rana za ta iya fakuwa kuma ita mai yi wa mijnta hidima ce ga mahaifinta da mijnta, inda sakamakon biyayyarta za ta haifi lafiyayyun ’ya’ya da zuri’a mai yawa da kuma samun jajirtacce da zai kula da zuri’arta. Akwai labarai da dama a cikin al’ummar da suke koya darasi na kin nuna wa makiyi muguwar kiyayya amma a riƙa gode wa makiyin domin in ba maƙiyin, ta yaya ne jarumai sunansu da matsayinsu za su ɗaukaka a cikin al’ummarsu?

By ukarofi