
Daga BELLO A. BABAJI
Ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya yi nasarar lashe zaɓen kujerar gwamnan jihar da aka yi a ranar Asabar.
Sakamakon da hukumar zaɓe, INEC ta fitar ya nuna cewa Okpebholo ya samu ƙuri’u 291,667 wanda ya ba shi damar doke abokin karawarsa na jami’yyar PDP, Asue Ighodalo wanda ya samu ƙuri’u 247,655.
Olumide Akpata na jami’iyyar LP shi ya zo na uku da ƙuri’u 22,763.
A ƙarƙashin haka, Okpebholo ya zama wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.
Kafin sanar da sakamakon, PDP sai da ta yi zargin an sauya sakamakon kamar yadda wakilinta na jihar ya bayyana inda ya nemi INEC a mataki na ƙasa ta yi bincike game da zargin.
