An halaka jagoran ƴan bindiga a Kaduna, Kachalla Tukur a musayar wuta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wata dabar ƴan bindiga ta yi nasarar kashe shahararre kuma Kwamandan ƴan bindiga, Kachalla Tukur Sharme a yayin wata ba-takashi a tsakanin su.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce an kashe Sharme ne tare da wasu ƴan dabarsa.

Aruwan ya ce, a lokacin da ɓangarorin biyu ke fafatawa, wasu mutane da aka yi garkuwa su sun samu nasarar tserewa daga komar ƴan ta’addar.

Ya kuma ce, akwai wasu daga cikin ƴan bindigar da suka samu raunuka, waɗanda a halin yanzu su na karɓar magani.

Lamarin ya auku ne a yankunan dazukan Rijana da Kaso da suka haɗe ƙananan hukumomin Kachia, Chikun da Kajuru.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, wasu daga cikin hare-haren da ƴan bindigar ke aikatawa sun haɗa da kashe-kashe da garkuwa da mutane a yankunan Millennium City, Maraban Rido da Kujama da kuma a ƙananan hukumomin Kagarko, Kachia da Birnin Gwari.

Har’ilayau, ayyukan ta’addancin Sharme kan faɗaɗa zuwa wasu yankunan jihohin Katsina da Neja.

Wata sanarwa da rundunar sojoji ta fitar a shafinta na X, ta ce ta dawo da muggan makamai bayan aukuwar lamarin.

By Babaji