Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Wasu rahotanni da aka yaɗa ta kafafen watsa labarai na nuni da cewa, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya koka da ƙarancin jami’an soja a ƙasar nan, duba da irin ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a sassa daban-daban, bayan ƙalubalen kuɗaɗen gudanar da ayyuka. An rawaito Babban Hafsan yana cewa, abu ne mai wuya sojojin da kaɗan suka wuce dubu ɗari ɗaya, su iya tsare rayukan ‘yan Nijeriya miliyan 200. Ba tare da ajiye wasu rarar jami’ai da za su gudanar da wani aikin kotakwana ba.
Babban Hafsan ya bayyana haka ne a Ilorin ta Jihar Kwara, yayin da yake gabatar da wata lacca game da gudunmawar sojoji da rawar da suke takawa ga cigaban ƙasa, albarkacin babban taron Cibiyar Nazarin Harkokin Zaman Lafiya da Zamantakewa da ke Jami’ar Ilorin. Taron da aka gudanar da shi tare da haɗin gwiwar Cibiyar Bada Horo Kan Dabarun Jagoranci da Samar da Zaman Lafiya ta Martin Luther Agwai, dake Jaji.
Ya ce, matuƙar ana son a cimma nasara wajen samar da ƙaƙƙarfar rundunar tsaro ta ƙasa tilas sai an ƙara yawan jami’an da ake da su da kuma ƙara yawan kuɗaɗen da ake ware musu, wajen sayen kayan aiki da gudanarwa. Sannan a ƙara ƙarfafa gwiwar ’yan ƙasa wajen marawa jami’an tsaro baya, da taimaka musu a yaƙin da suke yi da ɓatagari. Ta hanyar kafa ƙungiyoyin ‘yan banga masu aikin sakai, da za su riƙa aiki kafaɗa-da-kafaɗa da sauran jami’an tsaro, wajen bankaɗo maɓoyar ɓatagari da daƙile mugun nufinsu.
Tun bayan da Nijeriya ta koma kan tsarin siyasa na dimukraɗiyya, an riƙa samar da sauye-sauye da dama, da za su dace da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a ƙasar, da ma ƙalubale daga maƙwaftan ƙasashe. Wannan ne ya kai ga samar da wasu ƙarin rundunonin tsaro da za su rage wasu nauye-nauye da ke kan jami’an tsaro na soji da ‘yan sanda, irin su Hukumar Yaƙi da Almundahanar Kuɗaɗe ta EFCC, da Rundunar Yaƙi da Sha da Safarar Miyagun ƙwayoyi ta NDLEA, da kuma Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta DSS. Harwayau da Rundunar Tsaro Mai Kare Fararen Hula ta NSCDC, da kuma Rundunar Kiyaye Aukuwar Haɗurra ta FRSC. An kafa waɗannan hukumomi ne domin magance wasu muhimman buƙatun tsaro na ƙasa, da rage ɗimbin ayyukan da ke kan sauran rundunonin tsaro. Sai dai duk da haka, bai hana matsalolin tsaro da suke ƙara yawa a ƙasar nan a kowacce rana su ƙara yi wa jami’an ’yan sanda da sojoji yawa ba.
Babu mamaki shi ya sa wasu gwamnoni gabatar da buƙatar a basu damar kafa rundunar tsaro mallakar jihohi, domin ƙara ƙarfafa sha’anin tsaro a jihohinsu. Sai dai wannan buƙata tasu tana ta fuskantar turjiya, daga Majalisar ƙasa da wasu ’yan Nijeriya, saboda fargabar da ake da ita na cewa, ‘yan siyasa da gwamnoni za su iya amfani da rundunar tsaro ta jiha wajen murƙushe ’yan adawar su da ɓangarorin al’umma da ke da rashin jituwa da gwamnati. Wanda hakan ya saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasa, da makomar Nijeriya ta fuskar tsaro da zaman tare.
Samuwar ƙungiyoyin ’yan banga masu aikin sakai a jihohin yamma da na Arewa, ya taimaka wajen raguwar wasu matsalolin. Kodayake, ko su ma ɗin suna fuskantar matsalar rashin ƙwarewa, rashin wadatar kayan aiki, da kuma ƙarancin kuɗaɗe da alawus-alawus ɗin da ake biyansu. Domin duk da haka matsalolin tsaro ƙara bayyana suke yi. Kama daga kan rikicin manoma da makiyaya, ƙaruwar ƙungiyoyin masu tada ƙayar baya, ’yan ta’adda, ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane, ƙungiyoyin matasa ’yan daba masu sara-suka, da masu fashi da makami da sauransu. Yayin da ake cigaba da kama dubban makamai da albarusai, da ake shigowa da su ƙasar nan, ta ɓarauniyar, ko ma ake ƙera wasu a lunguna da cikin anguwanni ba tare da sanin jama’a ko jami’an tsaro ba. Sai dai idan dubu ta cika. Waɗannan na daga cikin dalilan da ke sa al’amuran tsaro ke ƙara damalmalewa a ƙasar nan.
Ba da jimawa ba ne, wasu rahotanni suka naƙalto Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa yana bayyana cewa, gwamnatinsa za ta bai wa jama’ar ƙauyukan da ke yawan fuskantar hare-haren ’yan bindiga makamai da horo, kan yadda za su iya kare kansu daga ’yan ta’adda kafin jami’an tsaro su kai musu ɗauki. Wannan ya biyo bayan kokawa da Gwamnan ya daɗe yana yi ne game da ƙarancin jami’an tsaro da za su kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.
A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta rawaito na ranar 11 ga watan Satumba, an jiwo Gwamna Dikko Raɗɗa cikin wata hira da ya yi da sashin Hausa na tashar rediyon ƙasar Jamus ta DW, yana cewa ‘yan sanda 32 ne kacal ke amfani da bindigogi 5 masu lafiya cikin 9 da ake da su, suna kare al’ummar da ke zaune a ƙauyuka 200 na Jihar Katsina. Kuma misalin hakan ne a mafi yawan jihohin ƙasar nan. Wannan ce tasa ’yan ta’addan daji suke cin karensu babu babbaka, a wasu yankuna na jihar.
Ya zama dole al’ummar ƙasa su shiga fargaba da tsoro jin irin kalaman da Babban Hafsan sojojin Nijeriya ya faɗa, inda a fili yana nuna gazawar rundunar tsaro ta sojoji wajen samar da tsaron da ake buƙata.
Shekaru bakwai da suka gabata na yi wata tattaunawa da wani tsohon babban jami’in ’yan sanda Marigayi Hamisu Ali-Jos, wanda ya ƙaddamar da wani gangamin kira ga gwamnatin wancan lokacin ta tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, don a samar da ƙarin jami’an tsaro da kayan aikin da za su taimaka musu wajen samun ƙwarin gwiwar tunkarar taɓarɓarewar tsaro a ƙasar nan.
Daga wannan lokacin Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta bayar da umarnin ɗaukar sabbin tsami’an tsaro har dubu 6 da za a zaɓo su daga dukkan ƙananan hukumomi 776 na ƙasar nan, domin ƙara inganta aikin tsaro. Wannan umarni da aka bayar da shi an nuna cewa zai riƙa aiki ne duk shekara, amma kuma hakan bata samu ba. Ko a ƙarƙashin wannan gwamnati ma an kawo irin wannan shawara dake buƙatar a ƙara ɗaukar sabbin ’yan sanda dubu 50 duk shekara domin samun ƙwarin gwiwar tunkarar matsalolin tsaron ƙasar nan.
Sai dai yaya batun sabbin sojoji na ruwa, da na sama, da na ƙasa, waɗanda alhakin tsaron rayukan al’umma da ƙasar bakiɗaya ke wuyansu? Lallai ya kamata magabatan mu su sake lale, tun kafin wankin hula ya kai su dare. Don muna ganin yadda ake fafatawa da ’yan bindiga a jihohin Zamfara, Sakkwato, Katsina, Neja da Kaduna, abin da ke nuna rashin wadatar kayan aiki da ƙarancin jami’an tsaro a ƙasa.
Sannan yana da kyau a ɓullo da wasu ƙarin rundunonin tsaron da za su riƙa taimakawa wajen sa’ido da yaƙi da ɓatagari, ko ƙarfafa gwiwar waɗanda ake da su a ƙasa, irin na ’yan banga na ɓGN, Neighbourhood Watch, Hisba, da ire-iren waɗanda jihohi suka kafa. Ko dai a dunƙule su waje guda a kafa musu wata rundunar, ko kuma a taimaka musu da horo da kayan aiki, kuma a ƙara inganta albashin su.
Allah Ya ba mu zaman lafiya a ƙasar mu Nijeriya.
