MAKAMASHI: Rayuwar wutar juyin juya-hali a makamashin fetur da gas

Spread the love

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI

“Wata daban” cewar kwaɗo yayin tsalle-tsallensa daga wannan ruwa zuwa ya yi tsalle ya faɗa kaskon tuyar arai, wato ƙosai, inji Malam Bahaushe, nan take ya yi waje ya furta wannan magana tasa, “wata daban”.

Tun lokacin da manya-manyan kamfanonin haƙar man fetur da fitar da shi waje su yi kasuwancinsa du ba mu la’ada, ’yan takarda a cikinmu tare da Turawa ’yan kasuwa daga UAC, GBO, CFO, BATAPZ da dai sauransu, duk ƙarshen mako su kira wo makaɗa da mawaƙa ’yan ‘highlife’ ga ruwan jiri da hajijiya a kwana ana kwankwaɗa da aka kawo daga Italiya da Faransa da kuma Potugal.

A waɗannan shekaru ne Shugaban ƙasa na wannan lokaci Janar Yakubu Gowon da ya sha dafe dagen san a karnuka da aladai da burkutunsa ta dawa mori ya ke shela wa duniya cewa, la’adar da kamfanoni irinsu Total, BP, SHELL, ESSO da AGIP, kafin haifuwar na Nijeriya irin Dahɓi Petroleum, Sahara Group, Intergrated Oil and Gas Ltd ko kuma su Conoil Plc and Gas Ltd cewa kuɗi ya yi wa Nijeriya yawa har ta rasa me za ta yi da kuɗi bayan matsaloli na jahilci, da rashin sanin ina muka dosa ga tsakanin talauci da yunwa da kuma rashin kwanciyar hankali, saboda bazuwar makamai a hannun matasa, domin ba a daɗe da gama yaƙin Biyafara ba.

Daga shekara ta 1953 da aka fitar da man fetur zuwa kasuwar duniya an fitar da ganga sama da tiriliyan 27. Kuɗaɗen sun isa har da rara da za a gina birane kamar Birnin Dubai na ƙasar UAE kamar 10 ko Makka da Madina a Ƙasar Saudiyya goma-goma ko kuma birane irin London, Paris, Madrid, Moscow.

Dukiyar da aka fitar za ta gina Birnin Bejing, Shanghai da Tokyo, haka idan ka tafi Amurka kuɗaɗen da aka kwasa daga Nijeriya za su gina Birane kamar Boston da New York da kuma Los Angles.

Amma abin takaici, a Nijeriya lokacin mulkin dimukraɗiyya da aka koya mana daga 1999 lokacin Obosanjo na PDP zuwa yau na Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima Muustapha na APC har yau ɗan Nijeriya, saboda jahilci bai san ya sanya sutura ba, a Jihar Zamfara da Kebbi da Naija da Taraba da Adamawa haka sama da ’yan ƙasar kashi 70 cikin 100 suna kwana ba su ci abinci.

Duk da cewa, tun 1912 ake kwasar dukiyar ƙasar nan ana fita da ita zuwa Yammacin Turai da kuma Amurka ta Arewa, wannan matsin rayuwa zai iya haifar da ruruwar wutar juyin-juya hali.

Idan ka na nazari kan koma-bayan Nijeriya daga 1960, wato shekaru 64 kenan da samun ’yanci da jam’iyyun siyasa na dauri irinsu A.G da NPC da NCNC da NEPU da kuma sauran ƙananan jam’iyyun suka ja ragamar samun ’yancin daga hannun gwamnatin Ingila.

Idan ba mu fitar da mafita ba a bana ba za mu samu kanmu kamar yadda manazarcin halin rayuwa mutumin Kano a wannan jarida ta Blueprint Manhaja, Ali Abubakar Sadiƙ, ya tunasar da mu kan rayuwar ’yan yawon shaƙatawa cikin jirgin ruwa na Titanic wanda suka ci karo da Iceberg, wato daskararriyar ƙanƙara, wacce ta kwashe sama da miliyoyin shekaru a ƙasan teku, ta fasa jirgin ruwan a teku cikin ƙanƙanin lokaci Ikon Allah ya haɗiye jirgin nan shi da kayan alatunsa.

Rashin imanin da ’yan Nijeriya, waɗanda muke kira talakawa da ’yan takardarsu da muke kira ‘elites’ sai kuma manyan masu hannu da shuni, wato fajiran ƙasar nan ga lafiya da kuɗi kuma ga mulki kuma su suke faɗa a ji a masana’antun man fetur na ƙasar nan kuma su na da muhimmiyar rawa a harkokin duniya, kamar yadda babban hamshaƙin attajiri a Afrika, Aliko ɗangote, ya kira su da ’yan mafiya.

Wallahi idan wuta ta kama a ƙasar nan sai ta fi duk wata wutar daji ta rikicin da tarihin ya kawo a wannan sarari na Subhana. Rikicin sai ya sauya taswirar mulki ta ƙasashen Turai, wato ‘European Union’, domin sun fi shekaru 200 suna zalintar wannan yanki na Afrika ta Yamma, bayan sun bi bayi sama da miliyan uku sun halaka, sun halaka wata miliyan ukun, saboda matsalolin sufuri na jiragen ruwa a tekun Atalantika. Daga mutane suka kwashi kayan amfanin gona kusan kyauta na biliyoyin daloli da foma-fomai zuwa masana’antunsu, suka kashe namu na gida.

Bayan sun ci duniya da dukiyarmu suka zo da aikin tilas na haƙar musu ma’adani kamar kuza da tama da azurfa da gwal, wato zinare da kuma lu’u-lu’u. Kuma kusan shekaru 40 kenan su na kwasar ɗanyen man fetur da gas da sauran dangoginsa, amma duk a ’yan la’ada mu ke, muna kwana cikin talauci da yunwa da cututtuka da babu wanda ya san mafarunsu.  

Wannan makon mako ne na warware hango wutar fitina dangane da zalincin da Yammacin Turai suke yi a ƙasar sama da shekara 200, kamar yadda muka zayyana a sama, amma rahoton da ya ke ta zagayawa a wannan makon cikin wannan jarida ta Blueprint Manhaja farashin man fetur daga shakara ta 1973 lokacin da ’yan Nijeriya suke biyan Kwabbai shida a duk lita guda da suka sha a gidan mai ba tare da wata tangarɗa ba. Bayan shekaru 51 farashin ya koma Kwabbai 120,000 kenan.

Daga Kobo shida ya koma Kobo 120,000, ka san masifa ta yi masifa, wato gobara daga kogi kashe ta sai waɗanda  suka kunna ta, waɗanda ba su wuce Ministan Albarkatun Man Fetur na ƙasata, Heineken Lokpobiri, da Babban Manajan Daraktah Rukunin Man NNPC, Kele Kyari, da Shugabannin ƙungiyar masu dillancin man fetur da ke ƙarƙashin shugabanta, Mista Billy Gillis- Harry, da ƙanwarta ƙungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (DAPPMAN). Wannan gobarar idan ta taso a wata mai kamawa, wallahi babu mai kashe ta sai wanda ya samar da makamashin da ku ke cin albarkacinsa.

Maganar gaskiya idan wutar ta koma, wallahi kamfanonin mai na Total, Mobil, Shell, ADIP da dai sauransu da suke karkaɗa muku garayar dujal, ba za ku gan su ba balle su kai ku maɓoya da suka gina da tsoron yaƙin makamin nukiliya. Wannan yaƙi ne na zalincin mutum da mutum, kamar yadda ake cewa, “mai tsoron ta mutu shi ya ke maho”. Kamar da hunturu ne, samari ’yan bana bakwai su tara bargonsu guda, wa zai haƙura? Amsa ita ce, mutuwar kasko.

Amma ga mutane masu hankali sun kawo magani da suka ce, kada a yarda a fara tun wuri a yi nesa da bakin wutar. Mai girma Shugaban ƙasa ya kafa tarihi da ya soke farashin man fetur da babu, wato ‘Zero Kobo’ Ka tambaye su daga 1953 zuwa 1973 kafin ya kai Kobo shida kowacce lita ta yaya suke sha har ma kuma Kobo shida su cire riba.

Domin kuwa tun daga wannan lokaci lita daidai ta ke lita ɗaya ko ɗigo ɗaya ba a ƙara ba. Masu saye sun ƙaru, masu fitar da shi wannan kaya sun ƙaru, amma farashi sai hauhawa ya ke yi. Wannan ya sa masu hankali suka ce, “idan har aka ci gaba matse ganga, za ta yi zaƙi, amma za ta fashe, babu sauran kiɗa.”

Shugaban NNPC, Malam Mele Kyari, idan ba so ka ke gangar Nijeriya ta fashe ba, ku ba wa Shugaban ƙasa shawara farashin man fetur ya koma kyauta ga ’yan Nijeriya ko kuma farashin da suka sani Kobo shida a shekara ta 1973, wanda kuɗi ya yi wa Najeriya yawa ta rasa yadda za ta kashe shi, inji Shugaba Janar Yakubu Gowon.

By ukarofi