Rashin tsaro: Sanata Yari da malaman Musulunci a Zamfara sun yi addu’a ta musamman wa Tinubu

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau 

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar ya shirya taron addu’o’i na ibada a ranar Talata tare da malaman addinin Musulunci na jihar Zamfara domin samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na nasarar yaƙi da ‘yan fashi a ƙasar nan. 

Sanata Yari a lokacin da yake buɗe taron addu’o’in a gidansa da ke garin Talatan Mafara hedikwatar ƙaramar hukumar Talata Mafara ya bayyana addu’o’in da aka yi wa gwamnatin Shugaba Tinubu a matsayin lokacin da ya dace don samun nasarar yaƙi da ‘yan ta’adda a ƙasar nan. 

A cewarsa, Nijeriya a karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na bukatar addu’a ga daukacin al’ummar musulmi a halin da ake ciki, inda rashin tsaro ya zama ruwan dare a wasu sassan kasar kan ayyukan ‘yan bindiga. 

“Ba mu da wani wurin rayuwa a Duniya da ya wuce kasarmu, don haka akwai bukatar dukkan ‘yan Nijeriya su rika yi wa shugaban kasa addu’a domin samun nasarar a yakin da suke da wadannan fitattun ‘yan ta’adda da suka addabi kasar”.  Yace 

A cewarsa, babu wata al’umma da za ta dore a inda babu zaman lafiya a kullum, yana mai jaddada cewa gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta kuduri aniyar ganin an samu zaman lafiya nan ba da dadewa ba a duk jihohin da abin ya shafa.

Wakilinmu ya tattaro cewa daruruwan limamai da malaman addinin Islama ne suka halarci zaman taron.

By ukarofi