Jam’iyyar APC ta kashe Nijeriya, yayin da ita kuma PDP ta mutu murus – Kwankwaso

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya caccaki jam’iyyar APC mai mulki a ƙarƙashin Shugaban ƙasa Bola Tinubu, inda ya bayyana cewa manufofinta sun ƙara ta’azzara talauci da yunwa tare da ƙara ta’azzara yanayin tsaro a ƙasar.

Kwankwaso, wanda ya bayyana haka a taron kwamitin zartarwa na ƙasa karo na 7 na jam’iyyar NNPP a Abuja ranar Litinin, ya kuma bayyana PDP a matsayin matacciyar jam’iyyar da ke fama da rikici a halin yanzu.

Yayin da ya bayyana jam’iyyar NNPP a matsayin jam’iyyar da ta fi kowace jam’iyya girma a Nijeriya, ya ce ita ce jam’iyya ɗaya tilo da za ta iya samar da shugabanci na gaskiya da zai magance buƙatun ‘yan Nijeriya da kuma kawo musu ɗauki.

“Jam’iyyarmu ta yi kyau sosai ta yadda mu a matakin shugabanci mun gamsu da ci gaban da muka samu.

“Kuma tabbas hakan zai kasance tare da hassada a wajen jam’iyyarmu, tare da kai hare-hare da dama daga ciki da ma wajen jam’iyyar.

“Na yi farin ciki sosai duk da ƙalubalen da ake fuskanta, a yau jam’iyyarmu, ita ce jam’iyyar da ta fi samun ci gaba a ƙasar nan.

“Na tuna lokacin da na ziyarci jihar Katsina domin buɗe ofishinmu na jihar, a can na bayyana cewa jam’iyyun biyu, musamman jam’iyyar PDP sun mutu kuma akwai damuwa da yawa a cikin jam’iyyar PDP.

“Na tabbata a lokacin da nake wannan furuci, da yawa daga cikinsu ba su ga abin da ke faruwa a yau ba wai ana yi jam’iyyar gunduwa-gunduwa, jam’iyyar na ta kururuta, don haka idan ba su fahimci wancan lokacin ba, to yanzu ina ganin za su yarda da mu duka cewa jam’iyyar ta mutu.

“Jam’iyyar APC kamar yadda take a yau, za ka ga cewa shugabanci na nan a sama, kuma al’ummar ƙasar nan baki ɗaya suna cikin kasa.

“A wannan matakin ko sun yarda suna yin kyau amma dukkan mu, musamman masu kada kuri’a a kasar nan mun yi imanin cewa suna tabuka abin kirki musamman idan aka yi la’akari da batun tsaro, matakin talauci a kasar nan kuma ba shakka. matsalar yunwa da muke gani a kasar nan.

“Don haka, mun gode wa Allah da cewa jam’iyyun biyu duk sun durkushe, jam’iyyarmu kuma NNPP ta hau. Mun gode wa Allah Madaukakin Sarki a kan haka,” in ji tsohon gwamnan.

By ukarofi