Nijeriya na neman hawa tsarin kama-karya na jam’iyya ɗaya – Atiku

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A yayin da Nijeriya ke bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar yayi kira da manyan ‘yan siyasa su haɗa kansu don kare dimukuraɗiyyar ƙasar daga hawa kan tsarin kama karya.

Atiku, a wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa, ya ambato cewa fannin siyasa na samun cikas a sannu a hankali a ƙasar nan a yayin da jam’iyyun adawa ke ƙara samun rauni a daidai lokacin da jam’iyya mai mulki ke haddasa wutar rikici a jam’iyyun don hana su tasiri.

ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar PDP a zaɓen da ya gabata, ya koka kan cewa Nijeriya na  neman zama mai bin tsarin jam’iyya ɗaya na kama karya, ya yi kira ga ‘yan siyasa da dattijan ƙasa da su tashi tsaye wajen ceto dimokuraɗiyya.

Jagoran ‘yan adawar ya ce, “A yayin da dimokaraɗiyya ke zama ado ga ɓangarorinmu a bisa matakan bin doka da oda, har yanzu ba mun kai matakin ci gaba ba na rainon tsarin siyasar bai wa kowa dama a dama da shi da kuma tabbatar da zaɓe na gaskiya”.

A don haka, ya yi kira ga jiga-jigan siyasa da su haɗa kai wajen kare dimokuraɗiyya daga kama karya.

“‘Yan mazan jiya sun haɗe kai kan buri guda, sun bada muhimmanci ga samun ‘yan cin gashin kan mu ta hanyar gwagwarmaya cikin lumana. Abin da muke murna a yau shi ne alkhairin da haɗin kansu ya samu da al’umomin da suka biyo bayansu,” inji Atiku.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya kuma taya ‘yan Nijeriya murna na cika shekaru 64 da samun ‘yanci.

By ukarofi