Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kungiyar Masu Buƙata ta Musamman a Nijeriya sun yi waiwaye kan inda aka kwana wajen kare haƙƙoƙi da kuma kyautata rayuwarsu a ƙasar.
Masu lalurar nakasa ko buƙata ta musamman sun yi waiwayen ne a yayin wani taro da suka gudanar a birnin Kano ƙarƙashin inuwar ƙungiyar ‘Northern Nigeria Disability Forum’ (NNDF).
A yayin taron, sun yi duba a game da abubuwa da dama ciki har da batun ilimi da lafiya da rabon tattalin arzikin ƙasa dama harkar zaman takewa.
Cikin abubuwan da suka gano shi ne har yanzu masu buƙata ta musamman ɗin na fuskantar matsaloli wajen harkar zamantakewa.
Shugaban ƙungiyar, Yarima Sulaiman Ibrahim, ya bayyana cewa, “Abin da muka lura shi ne har yanzu mutane ba su fahimci matsalar masu buƙata ta musamman ma bame ballantana su taimakesu, mutanen da suka fahimcemu aalilan ne.”
Yarima Suleiman Ibrahim, ya ce kundin tsarin mulkin ƙasa ya bayar da damar samun ‘yanci, amma a ɓangaren wannan ’yancin ba a la’akari da masu buƙata ta musamman.
“Ta fuskar walwala, masu buƙata ta musamman ba su da wannan ’yanci, domin a wasu jihohin Nijeriya kamar Legas da Abuja, ana yawan kama masu buƙata ta musamman a tozarta shi.”
Shugaban ƙungiyar ta NNDF, ya ce a wasu jihohin akwai wuraren da ake zuwa ana ajiye masu buƙata ta musamman wanda ɗan adam mai ‘yanci bai kamata aje a ajiye shi a wajen ba.
“Babbar damuwarmu a yanzu shi ne za ayi gyara a kundin tsarin mulkin Nijeriya, bamu da wakilci a wajen gyaran ballantana ma a san mene ne ma matsalarmu.”
Yarima Suleiman Ibrahim, ya ce “Ko shakka babu an samar da hukumar da ke kula da masu buƙata ta musamman, to amma har yanzu bata yin abin da ya kamata ace ta yi saboda har yanzu mutanenmu na bara a kan titi, to da ace hukumar na aikin da ya dace to ba za a ga masu buƙata ta musamman na bara a kan titi ba.”
“Babbar ribar da zamu ce mun samu ita ce faɗin albarkacin baki don yanzu kam muna da damar fadin albarkacin bakinmu, to amma sauran haƙƙoƙinmu ne muka rasa.”
Shugaban ya ce yanzu za su yi fito na fito da matsalolin da ke damunsu don su tunkaresu da gaske.
“Muna buƙatar ‘yan majalisun tarayya da sanatoci da su bar ƙofofinsu a buɗe saboda gyaran kundin tsarin mulkin ƙasa da za ayi yanzu muna so mu shigo ciki domin ayi damu, saboda a gyara abubuwa da dama da ke ci mana tuwo a kwarya kamar cin zarafi da kuma yadda ake yi mana kallo.”
“Mu yanzu abin da muke so hukumomi su yi mana shi ne a rinka duba me dokar kasa ta ce a bamu, domin dokar kasa ta ce duk wani abu da za a raba a bamu kashi biyar cikin 100, sannan kuma muna so gwamnatocin jihohi su samar da hukumomin da za su riƙa kula da buƙatunmu,” Inji shi.
