Haƙƙin jama’a ne kula da hidimar marayu, inji Uwar Marayun Jos

Spread the love

Daga HABU DAN SARKI a Jos

An bayyana muhimmancin nuna kulawa da tausayawa ga rayuwar marayu da ke cikin tsananin buƙatar taimako, musamman a halin rayuwa da jama’a ke ciki a ƙasar nan.

Shugabar Gidauniyar Tallafawa Mabuƙata da Zawarawa ta Alheri Danƙo Ne Charity Foundation, Hajiya Farida Shehu wacce aka fi sani da Uwar Marayu, ta nuna damuwa kan yadda wasu daga cikin jama’a ke nuna halin ko in kula da rayuwar da raunana a cikin al’umma ke ciki, musamman halin talauci da yunwa, da rashin kulawa ta ɓangaren lafiya da ilimi. 

Shugabar ta bayyana buƙatar hakan ne a wajen yaye wasu marayu da ‘ya’yan masu ƙaramin ƙarfi su fiye da 60 da suka samu horo kan sana’o’in dogaro da kai, ƙarƙashin ƙungiyarta ta Alheri Danƙo Ne Charity Foundation da ke Jos.

Ta ce, kodayake ƙungiyarta da taimakon wasu bayin Allah irin su babban malamin addinin Musuluncin nan na ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Iƙamatus Sunnah, Sheikh Abdullahi Bala Lau, da wasu masu hali a cikin Jos da kewaye, suna iyaka ƙoƙarin su wajen tallafawa da tausayawa mabuƙata, amma abin da ake bayarwa ba ya wadatarwa saboda yawan marayun da ake da su, da masu iyali da ke rayuwa cikin yunwa da talauci.

Ta yi fatan jama’a za su cigaba da tausayawa da abin da Allah Ya hore musu, don ciyar da marayu da nakasassu da zawarawa dake rayuwar hannu baka hannu ƙwarya, musamman a irin wannan lokaci da jama’a ke cikin ƙunci na tsadar rayuwa.

Wani fitaccen malamin addinin Musulunci da ke Jos, Sheikh Na’annabi Mu’azu wanda ya gabatar da nasiha a taron ya yi kira ga jama’a su riƙa tausayawa marayu da masu tsananin buƙata daga ’yan uwa da maƙwafta, duba da halin taɓarɓarewar tattalin arziƙi da ƙasar nan ke fuskanta. 

Shaihun malamin, wanda shi ne shugaban ɗariƙar ƙadiriyya na Jihar Filato ya bayyana cewa, addinin Musulunci yana ba da fifiko sosai kan al’amarin maraya, don haka ya buƙaci masu hali da ke cikin al’umma su riƙa tallafawa irin waɗannan ƙungiyoyi da ke ɗawainiya da rayuwar marayu da zawarawa.

Ya kuma yabawa shugabar wannan ƙungiya, Hajiya Farida Shehu bisa jajircewa da haƙuri da take nunawa wajen ɗaukar wannan hidima ta alheri, ba tare da gajiya ba. Sannan ya yi mata addu’o’in fatan alheri da samun nasarori masu yawa a rayuwarta, da sauran masu taimaka mata.

Wasu daga cikin mata da ‘yan matan da suka ci gajiyar shirin koyar da sana’o’in dogaro da kai, na ƙungiyar Alheri Danƙo Ne, sun bayyana farin cikinsu da jindaɗinsu na samun wannan dama, wacce suka ce ta basu zarafin koyon yadda ake yin man shafawa, man zafi, abin wuya na kwalliyar mata, da sinadarin wanki, da sarrafa kwamfiyuta. Sun ce a baya zaman kashe zani da talauci ya fara jefa rayuwarsu cikin wani hali, amma yanzu wannan sana’a da suka koya za ta basu damar neman na kansu da abin da za su kula da buƙatun su da na iyalinsu.

Wannan Gidauniya ta kuma taimakawa da ‘yan mata masu zaman kansu da matasa masu shaye-shaye, waɗanda suka yi alƙawarin canza rayuwarsu matuƙar sun samu mai jinƙansu da taimaka musu, yadda za su koma gidajen iyayensu, kuma su yi rayuwa tagari.

By ukarofi