Hukumar ‘yan sanda ta ƙasa ta bai wa jami’anta da suka mutu Naira 27.4 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan ‘yan sanda Aliyu Abubakar Musa ya miƙa kuɗi Naira miliyan 27.4 ga iyalan jami’an ta guda 36 da suka mutu a Katsina.

Da yake jawabi a bikin miƙa kuɗaɗen ga iyalan mamatan, kwamishinan ‘yan sanda a jihar Aliyu Abubakar Musa yace wannan kuɗaɗen an bada su ne ƙarkashin shirin inshora da ke ofishin babban sufeto na ƙasa.

Kwamishinan ya yaba
da ƙwazo da jajircewa da suka nuna a wajan aiki da ya jawo rasa rayukansu,yayi fatan Allah ya yi musu rahama.

Sai ya yi kira ga iyalan mamatan da suyi amfani da kuɗaden kaman yadda shirin ya tanadar ta hanyar inganta rayuwar ya’yan da suka bari a baya.

Najib shine yayi magana a madadin iyalan mamatan,ya godewa sufeton ‘yan sanda na ƙasa da kuma kwamishinan ‘yan sanda na jihar da irin ƙoƙarin da suka yi wajan samun wannan kuɗaɗen, ya kuma yi alƙawarin a madadin iyalan ‘yan sandan za su yi amfani da kuɗaden yadda ya dace.

Yawancin waɗannan yan sanda da sun rasa rayukansu ne a yayin da suke gudanar da aikin su .

By ukarofi