
Daga BELLO A. BABAJI
Bayan tseko da aka samu daga tuƙullumar wutar lantarkin Nijeriya a yammacin ranar Litinin, lamarin ya sake aukuwa a yau Talata inda miliyoyin al’umma suka shiga halin rashin wuta.
Kamfanonin raba wutar lantarki da dama a Nijeriya sun tabbatar da al’amarin wanda ya shafi kaso mai tsoka na al’ummar ƙasa.
Ɗaya daga cikin kamfanonin shine EKEDC dacke raba wa mutanen Jihar Legas lantarki kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X inda ya sanar da kwastomominsa tare da basu haƙuri game da hakan.
Kawo yanzu dai ana cigaba da ƙoƙarin ganin an warware matsalolin da suka haddasa hakan kamar yadda AEDC (na Abuja) ya bayyana.
Sauran kamfanonin da suka tabbatar da batun sun haɗa da na jihohin Kaduna da Enugu waɗanda ke raba wa mutanesu da ma na wasu jihohin.
