


Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira ga sabbin daraktocin hukumar zuba hannun-jari ta ƙasa, NSIA da su faɗaɗa guraben zuba hannun-jari don taimaka wa ɓangarorin harkar tattali a Nijeriya.
A lokacin da ya ke ganawa da daraktocin a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, Shettima ya zayyano ababen da gwamnatin tarayya ta shirya bai wa hukumar don bunƙasa ayyukanta musamman ta fuskar ƙarfi a ɓangaren kuɗi.
Ya kuma nuna buƙatar NSIA ta bada tallafi ga harakar tattali a ɓangaren harkar noma da inganta shi, ya na mai kira a gare su da su ɗore akan hakan.
Ya ce, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta cigaba da taimakawa wajen ganin an cimma manufofin gina ƙasar tare da yin aiki hannu-da-hannu.
A nasa jawabin, Shugaban tawagar daraktocin, Mista Segun Ogunsanya ya ce ziyararsu zuwa Fadar abu ne da ya ke da muhimmanci don gabatar da kansu ga mataimakin shugaban ƙasar inda ya miƙa godiyarsa ga Shettima da kuma mambobin Majalisar Tattali ta Ƙasa, NEC.
Ya kuma tabbatar da cewa za su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da adalci musamman kan yadda aka kafa hukumar NSIA, kamar yadda ya bayyana a madadin takwarorinsa.
