Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Ƙungiyar masu sana’ar sayar da iskar gas ta ƙasa reshen Jihar Kano ƙarƙashin shugabancin Kwamared Omede Mohammed, na buƙatar tallafin gwamnatin Kano ƙarƙashin shugabancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, Gwamnan Kano da kuma gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin shugabancin Asiwaju Ahmad Bola Tinubu, domin ta ci gaba da ɗaukar matasa aiki da kuma horar da su irin wannan sana’a da ake tsananin buƙatarta a ko’ina, kasancewar al’umma ta dogara ne da wannan sana’a wajen girkin abinci da kuma sarrafa wasu kayayyaki na amfanin yau da kullum da ake yi da gas kamar dai yadda shugaban ƙungiyar ta Petroleum Gas Retailer Branch Of NUPENG reshen Jihar Kano da ake kira da PGR a taƙaice ƙarƙashin shugabancin Kwamared Omede Mohammed a Kano.
Haka kuma ya ce wannan ƙungiya yanzu haka ta samawa ɗaruruwan matasa aikin yi a Kano ta yadda duk wani shago na sayar da tukunyar gas ko ɗura gas, ba za a ga mutum ɗaya ba ko sama da haka, wannan shi ne ya sa suke buƙatar tallafi daga gwamnatin jiha da ta tarayya domin su cigaba da tallafawa matasa ta hanyar horar da su da ɗaukar su aiki a guraren da ake sana’ar a cewar Omede.
A ƙarshe ya ce a matsayin shi na shugaba da aka zaɓa a samu nasarori a masu yawa a wannan ƙungiya kuma akwai buƙatar a samu haɗin kai, domin cigaban wannan ƙungiya wacce ta ke tsaye wajen bin doka da oda na sharuɗan wannan sana’a da al’umma da dama ke cin gajiyar ta a Kano da ma Nijeriya baki ɗaya.
