Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara Hajiya Hurriyya Dauda Lawal a ranar Laraba ta jagoranci dubban mata da masu ruwa da tsaki a jihar wajen taron tattaunawa kan cin zarafin mata da yara ƙanana, tare da jaddada buƙatar dake akwai wajen haɗa ƙarfi da ƙarfe don kawo ƙarshen cin zarafin mata da yara marasa galihu a jihar ta Zamfara.
Taron ya kasance wani ɓangare na fafutuka na kwanaki 16 don tunawa da ranar cin zarafin mata na shekarar 2024 a jihar.
Shirin bada agaji na sa kai tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Zamfara ne suka shirya bikin tunawa da ranar cin zarafin mata da yara ƙanana na tsawon kwanaki 16 akan cin zarafin mata.
Taken taron na bana shi ne “Faɗakarwa domin kawo ƙarshen cin zarafin mata”.
A nata jawabin, uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Hurriyya Dauda Lawal, ta bayyana cewa gwamnatin mijin ta za ta yi duk mai yiwuwa wajen yaƙi da duk wani nau’i na cin zarafin mata musamman yadda yake shafar mata da ƙananan yara marasa galihu.
A cewarta, gwamnatin jihar na haɗa hannu da duk masu ruwa da tsaki wajen yaƙi da cin zarafin mata da ƙananan yara a jihar.
Ta yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da cin zarafin mata da ƙananan yara zai fuskanci hukunci mai tsanani, ba tare da la’akari da asalinsa ko muƙaminsa ba a jihar.
Hajiya Hurriyya Dauda Lawal ta ci gaba da cewa nan ba da jimawa ba za a fara aiwatar da dokar hana cin zarafin jama’a a jihar, don kare haƙƙin yara da mata masu rauni da tare da ba da kariya da magunguna ga waɗanda abin ya shafa, da kuma hukunta waɗanda suka aikata laifin.
Idan dai za a iya tunawa majalisar dokokin ƙasar nan ce ta amince da dokar ta VAPP, sannan kuma Shugaba Goodluck Jonathan ya sanya wa hannu a ranar 25 ga watan Mayun 2015.
An kuma ƙirƙiro wannan dokar ne domin mayar da martani ga yawancin laifukan cin zarafi da cin zarafin bil’adama a Nijeriya, da suka haɗa da, fyaɗe, nakasa ma’aurata, korar tilas daga gida, tilastawa, kisa da sauransu.
