Daga MUKHTAR YAKUBU
A ci gaba da tattaunawa da jaruma kuma darakta a masana’antar finafinai ta Kannywood, Mansurah Isah, mai karatu zai ji yadda take son ta amfanar da matan Kannywood daga tallafin da NITDA ta ba su, don ganin sun tsayu da ƙafafunsu ta yanda ko shahara ta yi masu kaye suna da madogara da za ta hana su shiga mawuyacin hali.
Idan mai karatu na biye da mu, kuma bai manta ba, mun fara tattaunawa da jaruma Mansurah kan yadda ta samu wannan tallafi, da kuma yadda matan Kannywood ke shiga mawuyacin hali yayin da suka bar fitowa a matsayin jarumai, ko suka yi aure, dalilin rashin wata sana’a a gefe wadda za su iya yi ko bayan an bar yayin su. Sannan ta yi mana bayyanin yanzu haka abinda suka nema daga hukumar ta NITDA, ta cika masu alƙawari, domin kayansu har sun iso hannunsu.
Idan kun shirya, ga ci gaban tattaunawar.
MANHAJA: Da yake harkar ta mata ce ko ta wacce hanyar matan Kannywood za su ci moriyar wannan tallafin?
MANSURAH ISAH: To mun shirya samar da aikin yi ga mata da kuma wayar musu da kai mu nuna musu cewa a matsayin su na matan Kannywood akwai hanyoyin dogaro da kai ga mace ko da ta yi aure wadda a yanzu mun samar da wasu ƙwararru da za su bayar da horo a han hakan, don haka za a rinƙa horas da mata da matasa, ba wai mata kaɗai ba su ma matasa za mu horas da su ta yadda su ma za su samu hanyar dogaro da kai.
Don haka muna albishir ga duk wata mace da take son ta koyi wani abu na kasuwancin zamani da sana’a a cikin harkar fim ta fanin soshiyal midiya kamar YouTube, Instagram da sauran manhajoji da suke samar da kuɗi ba tare da mace ta fita daga cikin gidan ta ba. Sannan ya za ta koyi harkar tacewa da kuma sarrafa hotunan fim ta yadda tana zaune a cikin gidanta za a rinƙa kawo mata, kuma ka ga muna da ƙarancin mata a ɓangaren tace finafinai don haka ake ganin kamar duk harkar maza ce, kuma su maza ba su cika mayar da hankali kan abin ba don ko ni akwai fim ɗin da sai asarar sa na yi a wajen waɗanda na bai wa aikin, saboda ba su da wani takamaiman wajen zama. Don haka za mu yi amfani da wannan kaya wajen magance irin waɗannan matsaloli.
Wannan harkar bayan kayan da kuka samu tana buƙatar kuɗin tafiyar da ita. Ko akwai wani tsari da kuka yi na samun kuɗaɗen gudanar da ita?
E to muna ta ƙoƙarin samar da hanyoyin, amma dai a yanzu abin da yake hannun mu da shi za mu fara kamar yadda muka yi ƙoƙarin samun kayan haka ma kuɗin gudanarwa za mu nema kafin zuwa lokacin da wajen zai iya riƙe kansa, duk da dai mun ce yawancin abubuwan da za mu rinƙa koyarwa a wajen kyauta ne, amma za mu yi ƙoƙarin samar da hanyar da wajen zai iya riƙe kansa yadda za mu rinƙa biyan ma’aurata da sauran ayyukan gudanarwa na yau da kullum.
Kamar yadda kika sani ne duk wata mace idan ta shigo harkar fim burinta shi ne zama jaruma. Ko wacce hanyar za ku bi wajen nuna musu cewa ba aktin kawai ba ne sana’a a cikin harkar fim?
To na farko dai ina jin a cikin sa’anni na da muka shigo harkar fim, ina ga kusan ni ce a cikin harkar fim ɗin gabaɗayan rayuwata wata ban fita ba har yanzu kuma mata suna kallo na suna alfahari da ni saboda sunana na Mansurah Isah bai ɓace ba, tun da na shigo harkar babu wani darakta ko furodusa da nake bi don ya samo mini wata hanya. Duk da a yanzu ba wani fim nake yi ko, ko da idan ta ɗauro nan gaba za a ganni a cikin fim ana gani na da mutunci saboda ni nake nemowa na yi da kaina , don haka mata su sani idan babu aktin akwai zama furodusa ko darakta ko ɗaukar hoto da dai sauran su. Don haka ba sai da aktin kawai za a samu kuɗi ko ɗaukaka a cikin harkar fim ba , domin hakar ta na da faɗi sosai. Yanzu idan za a yi fim sai ka ga mutanen da za a ɗakko sun linka jaruman da za su fito a cikin fim ɗin sau uku ko sau huɗu, don sai ka yi fim da jarumai ashirin, amma sai ka ga ma’aikatan sun fi hamsin, tun daga kan masu rubutun labari har zuwa masu tace hotunan fim cin idan an kammala har zuwa tallan fim ɗin da kuma sakin sa a kasuwa. To amma me ya sa mu mata za mu tattara mu ce sai aktin kawai, wannan ba daidai ba ne kuma za mu yi iya yin mu wajen wayar da kan mata a kan wannan tunanin da suke da shi.
Saƙonki na ƙarshe.
Saƙona na ƙarshe ina so na yi amfani da wannan dama wajen isar da saƙona ga National Information Technology Development Agency, NITDA, a kan yadda suka taimaka wa masana’antar Kannywood a matsayina na mace da suka ba ni wannan tallafin don ganin masana’antar Kannywood ta amfana kuma ina mai tabbatar da cewa za mu yi amfani da wannan dama da muka samu wajen ciyar da masana’antar Kannywood gaba. Mun gode muna ƙara godiya sosai. Kuma in sha Allah za mu ci gaba da wayar da kan mata a kan fasahar ci gaban zamani da kuma koyar da su yadda su ma za su zama abin alfahari ba wai kawai su tsaya a matsayin aktin kawai ba, wanda daga lokacin da aka daina yayin su kuma rayuwar ta tsaya kenan.
To madalla mun gode.
Ni ma nagode sosai.
