Autar marubuciya Bushira Nakura ta yi saukar Al-ƙur’ani Mai Girma

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Aisha Gali Suleiman wacce aka fi sani da Nasreen, ɗiya ce ga fasihiyar marubuciya Hajiya Bushira Aminu Nakura, kuma auta a cikin ‘ya’yanta. Aisha Nasreen cikin yardar Ubangiji ta samu damar sauke sittin ɗin nan ta Al-ƙari’ani Mai Tsarki, wanda kafanin ɗiyoyin Musulmi ke fata da kuma mafarkin hakan. Saukar dai ta Aisha Nasreen ta yi shi ne a matakai biyu, wato ajin biye da kuma na hadda, wanda ta yi dukka wannan karatu ne a ‘Madasatul Mu’assasa’ da ke gidan Khalifa Isyaka Rabi’u (Khadimul ƙur’an) da ke Gwauron Dutse. Ashe ke nan ma iya cewa Aisha Nasreen da abokan karatunta sun kwankwaɗi madarar karatun na Al-ƙur’ani daga ahalin Al-ƙur’ani. Allah Ya ba mu albarkar masu albarka Ameen.

An yi bikin yaye ɗaliban da suka yi wannan sauka ne dai ta su Aisha Nasreen ranar Lahadi 17/11/2024 a harabar wannan makaranta ta Mu’assasa da ke gidan Khadimul ƙur’an Marigayi Khalifa Isyaka Rabi’u, tare da miƙa musu allunan sauka da kuma takardar shaida da hukumar makarantar ta rabawa ilahirin ɗaliban da suka samu nasarar shiga ajin wannan sauka na biye da kuma na hadda a kowanne mataki. Wanda Aisha Nasreen ta samu takardun shaidar har guda biyu wato na biye da kuma na hadda, domin tasamu haddace izufi 30, inda ta karɓi wani allon na ɗan hadda aranar 1/12/2024

Bayan makaranta ta yi nata bikin saukar a ranar 17/11/2024. Mahaifiyar Nasreen wato marubuciya Bushira Aminu Nakura wacce memba ce a ƙungiyar marubuta mata zalla ta ‘Mace Mutum Writers Association’ kuma marubuciyar littafin ‘Tukunyar Zamani’ ta shirya wa ɗiyar tata walimar taya murna a ranar Lahadin da ta zagayo wato 24/11/2024, a gidanta da ke unguwar Dukawa. Walimar da marubuta da dama suka samu halarta.

Lokacin da wakilinmu ya tambayi Nasreen, ko me za ta ce game da wannan sauka da ta yi? Cikin mayalwaciyar fara’a da murmushi a fuskarta wanda ke nuna maɗaukakin farin cikin da take ciki ta amsa da cewa: “Ba ni da abun cewa ban da na godewa Allah Ubangijin Musa da Haruna, wanda Ya azurtani da mahaifiya tagari jajirtacciyar uwa, da kuma dukkan yayuna da suka tsaya kai da fata ganin sun kula da karatuna, da tarbiyyata, da kuma walwalata. Domin kuwa da bazarsu ce nake taka rawata, haka da ƙoƙarinsu ne nake cimma dukkan nasarori a rayuwata. Allah Ya ƙara musu lafiya da nisan kwana kuma Ya albarkaci nemansu Amin. Haka kuma dole na ƙara gode wa malamanmu da suka yi tsayin daka wajen ba mu ilimi mai amfani da kuma ɗora mu bisa tafarki madaidaici. Allah Ya saka musu da aljanna Amin. A ƙarshe zan yi amfani da wannan dama na yi kira ga ‘yan mata har ma da samari, a kan su yi watsi da rayuwar shashanci da girman kai, su kuma makaranta su rungumi karatun addini, wanda shi ne mafita da zai kai mu ga tudun mun tsira a ranar  gobe ƙiyama. Su sani dai cewa, ba a girma da karatu musamman ma karatun sanin Ubangiji Mahalicci. Allah Ya ganar da mu gaskiya Ya sa ƙur’ani Ya cece mu, Amin.”

By ukarofi