Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore ya bayyana aniyarsa na inganta haɗin gwiwar da ake yi da hukumar gidan talabijin ta Nijeriya (NTA) domin ƙara danƙon zumunci.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar a ranar Laraba ya yabawa NTA bisa rawar da take takawa wajen samar da sahihan bayanai akan lokaci da suka yaɗu a faɗin Nijeriya. An amince da NTA saboda gagarumin tasirin da take da shi wajen tsara tunanin ‘yan Nijeriya da kuma bayyana kyawawan al’amuran al’umma ga masu sauraron duniya.
A yayin ziyarar, Alhaji Sani Yusuf Hanga, wanda Babban Manajan NTA Kano ne, ya bayyana irin nasarorin da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta samu a ƙarƙashin jagorancin Kakakin majalisar Jibril Ismail Falgore tun bayan hawansa mukamin.
Sani Hanga ya jaddada daɗaɗɗiyar alaƙar haɗin gwiwa tsakanin NTA da majalisar dokokin Kano a matsayin mai matuƙar kyau da ƙarfafa gwiwa. Ya kuma tabbatar wa Majalisar cewa NTA ta jajirce wajen ganin an ɗore da wannan haɗin gwiwar.
Haɗin kai tsakanin NTA da Majalisar Kano na da nufin haɓaka dabarun sadarwa da yaɗa bayanai don cin moriyar juna.
Daga cikin tawagar ta NTA ta haɗa da Manajan Darakta Sani Yusuf Hanga da Mataimakin Daraktan Injiniyoyi da mataimakin daraktan shirye-shirye Mal. Shuaibu Garba Dakata, da sauran jami’ai.
