Daga USMAN KAROFI
Wata mummunar gobara da ta tashi a kasuwar Masaka, da ke ƙaramar hukumar Karu a Jihar Nasarawa, ta bar ‘yan kasuwa da yawa cikin alhini, suna ƙidaya asararsu.
A cewar shaidu, gobarar ta fara ci ne misalin karfe 10 na daren Juma’a, tana mai lalata bangarori da dama na kasuwar. Har zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoton, babu jami’an kwana-kwana da suka isa wajen domin shawo kan gobarar, yayin da wasu sassan kasuwar ke ci gaba da ƙonewa.
Wannan shine karo na farko tun shekarar 2019 da irin wannan gobara ta afku a kasuwar. Bidiyoyin da Blueprint Manhaja ta samu sun nuna ‘yan kasuwa suna bayyana asararsu yayin da wasu ke bincike a cikin toka domin neman kayayyakin da za su iya tsira da su.
A halin yanzu, ‘yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati da ta kawo musu ɗauki domin rage raɗaɗin wannan babban asara.
