Bankin Duniya ya amince da sakin bashin dala biliyan 1.5 ga Najeriya, bayan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar da wasu sauye-sauyen tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur da ƙara wasu haraji.
Bashin, wanda ke cikin shirin “Reforms for Economic Stabilisation to Enable Transformation”, an fitar da shi cikin ƙanƙanin lokaci, inda aka saki kaso na farko na dala miliyan 750 a watan Yuli, yayin da aka saki kaso na biyu a watan Nuwamba 2024.
Duk da haka, matakan sun haifar da ƙaruwar tsadar rayuwa ga ‘yan Najeriya, yayin da farashin man fetur ya ninka sau biyar, kuma hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 34.60 cikin 100.
Sai dai gwamnatin ta ƙaddamar da tallafi, amma mutane ƙasa da miliyan biyu ne suka amfana.
Har ila yau, shirin amfani da iskar gas mai rahusa don rage raɗaɗin cire tallafin man bai kai matakin aiwatarwa ba. Wannan ya bar ‘yan Nijeriya da cunkoson matsalolin tattalin arziki da hauhawar farashi.
