Daga BELLO A. BABAJI
Wani abin fashewa da ake kyautata zaton bom ne ya tarwatse a wata makarantar Islamiyya dake garin Kuchibiyu a ƙaramar hukumar Bwari dake birnin tarayya Abuja wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ɗalibi guda ɗaya na raunata wasu huɗu.
Lamarin ya auku ne a ranar Litinin 6 ga watan Junairu, inda ya haifar da tashin hankali acikin al’ummar garin dake da nisan kilomita 42 daga ƙwaryar birni.
Tuni tawagar bada agajin gaggawa ciki har da jami’an ƴan sanda dake lalata bom suka garzaya wajen da abin ya faru inda suka hanzarta kai waɗanda suka samu raunuka asibiti.
Wata majiya daga jami’an tsaro ta ce ɗalibin da ya rasa ransa wanda ba a bayyana kowaye ba, an gan shi ɗauke da wani abu da ake tsammanin abin fashewa ne gabannin faruwar lamarin.
Ba a samu wakili daga makarantar ko mai magana da yawun ƴan sandan Abuja, Josephine Adeh ba a lokacin haɗa rahoton.
