Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A ƙoƙarin ta na samar da gine gine a makarantun firamare a faɗin jihar, gwamnatin Dikko Raɗɗa ta kashe Naira biliyan 5 wajen gina makarantu 150 a faɗin jihar.
Mataimakin gwamnan jihar Farouk Lawal Joɓe ya sanar da haka a hira da manema labarai a Katsina.
Yace banda gina makarantu akwai gyara wasu da gina azuzuwa da gyara waɗanda suka lalace .
“Akwai samar da lantarki mai amfani da hasken rana,gina rijiyoyin burtsatse haɗi da tankunan su” inji Joɓe.
Mataimakin gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta gina masashe da ɗakunan ajiya na makarantun.
Joɓe ya bayyana cewa wannan mataki da gwamnati ta ɗauka na gina tare da gyara makarantu ya haifar da kyakkyawar sakamako wajen inganta koyo da koyarwa a matakin ilimin firamare a jihar.
Bayan haka ya ƙara da cewa gwamnati Dikko Raɗɗa ta rarraba bauta guda 70 ga jami’ai masa tabbatar da ingancin ilimi a faɗin jihar. Ya ce.
“Waɗannan jami’ai su ne zasu kula tare da tantance ingancin a makarantu da ke faɗin jihar”mataimakin gwamnan ya ƙara da cewa.
