Daga RABIU SANUSI a Kano
Shugaban ƙaramar Hukumar Tarauni, Alh. Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure, ya jagoranci ƙaddamar da shirin duba lafiyar jama’a kyauta tare da bayar da magunguna ga sama da mutane 2,000 a asibitin Babbangiji da ke yankin ƙaramar hukumar Tarauni.
Wannan na ɗauke ne a wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Tarauni ya fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta ce shugaban ƙaramar hukumar Tarauni Alh Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure wannan shiri na daga cikin manyan ayyukan da ya aiwatar domin bikin cikarsa kwanaki 100 akan kujerar shugabancin ƙaramar hukumar Tarauni.
A yayin ƙaddamar da shirin, wanda aka gudanar a asibitin Babbangiji da kuma sauran cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban a yankin domin duba lafiyar al’umma tare da yi musu gwaji cututtukan dake damunsu da kuma ba su shawara daga ƙwararrun likitoci, da ba su magungunan kyauta.
Shugaban ƙaramar hukumar ya jaddada cewa wannan mataki wani ɓangare ne na ƙudirinsa na samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Tarauni, musamman marasa ƙarfi da ke buƙatar kulawa ta musamman.
Haka kuma ya yi godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da kwamishinan ƙananan hukumomi na jihar Kano Alh Tajo Othman Zaura bisa gudunmuwar da suke ba su wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa a faɗin yankin ƙaramar hukumar Tarauni.
A jawabinsa a yayin ƙaddamar duba lafiyar kyauta da shugaban ƙaramar hukumar Tarauni ya samar a yankin mai bai wa Gwamna shawara kan ƙungiyoyi masu zaman kansu na jihar Kano Alh Nasiru Isa Jarma Tarauni, ya ce shi ma zai cigaba da yin iyaka iyawarsa wajen tallafawa shugaban ƙaramar hukumar Tarauni domin ya cigaba da tallafawa al’ummar yankin daga nan ya yi kira ga waɗanda suka amfana da duba lafiyar kyauta da su tabbata sun yi amfani da magungunan ta hanyar da ta dace.
Shugabar sashin lafiya ta ƙaramar hukumar Tarauni Hajiya Saratu ta yaba wa shugaban ƙaramar hukumar Tarauni Alh Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure bisa yadda yake ƙoƙari wajen inganta harkokin kula da da lafiyar al’ummar yankin musanman wajen kula da tsaftar muhallin.
A yayin ƙaddamar da duba lafiyar al’ummar kyauta shugaban ƙaramar hukumar na tare da kansilolinsa da masu ba shi shawara.
