Ɗanjuma da Ɗanjummai? Rikicin Akpabio da Natasha ya janyo ayar tambaya

Spread the love

*Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha bayan da ta sake shigar da ƙorafinta

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Biyo bayan tashin saɓani tsakanin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da Sanata Mai Wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti Uduaghan, inda suka zargi juna da aikata abubuwan da ba su dace ba, binciken tarihi ya nuna cewa, akwai ayar tambaya akansu bisa la’akari da abubuwan da suka gabata a baya. Ta zarge shi da neman yin lalata da ita, yayin da shi kuma ya zarge ta sharara ƙarya, zarge-zargen da dukkaninsu ba su da tabbas, idan aka yi la’akari da tarihinsu.

A 2014 Natasha ta taɓa zargin Reno Omokri, tsohon Mai Taimaka Wa Shugaban ƙasa na Musamman, da neman yin lalata da ita, amma a ƙarshe ta cire bayanan daga shafinta, sannan ya ce an biya shi diyyar ɓata masa suna. Shi kuma Akpabio, tsohuwar Manajar Darakta ta Hukumar Raya Yankin Neja Delta, Joy Nunieh, ta yi zargin ya nemi yin lalata da ita, amma ya ƙaryata. Sai dai kuma bai nemi haƙƙin ɓata masa suna, kamar yadda Omokri ya yi ba.

A jiya Alhamis ne dai, Majalisar Dattawan Nijeriya ta ɗauki matakin dakatar da Sanata Natasha har na tsawon watanni shida bisa shawarwarin da Kwamitin ɗa’a, Ladabtarwa da Sauraron ƙorafi na majalisar ya bayar bayan gudanar da bincike da nazari kan zargin da aka yi wa sanatar na karya tsarin ƙa’idojin aiki a majalisar.

Wannan ya biyo bayan samun nasarar da Sanata Natasha ta yi ne wajen sake shigar da ƙorafi kan zargin cin zarafinta ta hanyar neman lalata da ita da ta ce Shugaban Majalisar Dattawar, Sanata Godswill Akpabio ya yi mata, zargin da shi kuma ya ƙaryata.

Shugaban kwamatin, Sanata Neda Imasuen, ne ya bayar da shawarwarin bayan karanto jerin laifuka da kwamitin ya ce ya samu Sanata Natasha da aikatawa a majalisar.

Yayin da ya ke karanta bayanin dakatarwar, Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, wanda a kansa ne Sanata Natasha ke ƙorafin cin zarafi na lalata, ya nemi jin ra’ayin ’yan majalisar kan su amince ko su ƙi amincewa da dakatarwar ta tsawon watanni shida, amma kuma za a iya rage yawan lokacin idan har ta rubuto takardar neman afuwa. Nan take ’yan majalisar kuma sun amince da hakan.

Da ma dai tunda farko, a ranar Laraba, sai da kwamitin na ɗa’a, Ladabtarwa da Sauraron ƙorafin Jama’a na Majalisarya yi watsi da ƙorafin Sanata Natasha bisa dalilan cewa, ƙorafin da Sanata Natasha ta shigar ranar Laraba bai cika ƙa’ida ba, saboda ita mai ƙorafin da kanta ta sanya hannu kan ƙorafin maimakon ta bai wa wani ya shigar da shi a madadinta, lamarin da ya ce ya lalata ƙorafin nata tun ba a je ko’ina ba.

Ya kuma ƙara da cewa, batutuwan da ke cikin ƙorafin suna gaban kotu a yanzu haka, wanda ya sa ba za a iya tattauna su ba kuma majalisar ba ta da hurumin sauraron su.

Kafin dai Shugaban Majalisar ta Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da dakatar da Sanata Natasha sai da aka bai wa ’yan Majalisar Dattawan da dama sun tofa albarkacin bakinsu inda ba tare da ragin ɗaka ba suka goyi bayan hukuncin.

Sai dai Shugaban Marasa Rinjaye Na Majalisar Ta Dattawa, Sanata Patrick Abba Moro na jam’iyyar PDP, wanda shi ma ya ƙwanƙwashi Sanata Natasha, amma ya nemi majalisar ta yi wa ’yar majalisar sassauci, inda ya ce, a rage tsawon lokacin dakatarwar daga watanni shida zuwa uku.

Sanata Natasha ta miƙe a fusace ta ce, “wannan rashin adalci ba zai zore ba!” kafin a kashe abin maganarta, kuma Sajen Majalisa ya iza ƙeyarta zuwa waje.

Tun kafin faruwar hakan, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta sake gabatar da koken cin zarafi akan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a yayin zaman majalisar.

Ku tuna cewa a ranar Larabar da ta gabata ne Sanatar Kogi ta Tsakiya ta gabatar da irin wannan ƙara wanda ya haifar da cece-kuce.

Shugaban Kwamitin ɗa’a na Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Monguno (APC, Borno ta Arewa), ya yi tsokaci akan lamarin, inda ya yi misali da Doka ta 40 a Majalisar Dattawa.

Ya ƙara da cewa, ba za a iya sauraron ƙorafin ba, domin kotu tana sauraron batun da ta shafi Sanata Akpoti-Uduaghan da Ekaette Akpabio, uwargidan Shugaban Majalisar Dattawa.

Monguno ya kuma ƙara da cewa, ba za a iya la’akari da koken ba tunda ita Sanata Akpoti-Uduaghan da kanta ta sanya hannu a kansa, saɓanion tanadin dokar majalisar, wacce ta ce ɗan majalisar ba zai iya shigar da ƙorafi da kansa ba, sai dai wani daga waje.

Sakamakon haka, kwamitin ɗa’a na majalisar dattawa ya yi watsi da buƙatar, inda ta bayyana ta “mutu ne da isowarta”.

Sai dai a jiya Alhamis ɗin Natasha ta gabatar da buƙatar a madadin mutanen mazaɓarta ƙarƙashin jagorancin wani mai suna Zubairu Yakubu.

Bayan gabatar da koken, Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio ya tambayi ko akwai wasu cikas a shari’a na karɓar koken. Sanata Akpoti-Uduaghan ta amsa cewa, babu ko ɗaya. Da ƙarfe 12:38 na rana, Akpabio ya umarce ta da ta gabatar da buƙatar a gaban Majalisar Dattawa.

Daga nan ne aka miƙa koken ga kwamitin majalisar dattawa kan ɗa’a da ƙorafi a ƙarƙashin jagorancin Sanata Neda Imasuen (LP, Edo ta Kudu) tare da bayar da umarnin komawa da cikakken sakamako ga zauren majalisar a cikin makonni huɗu bayan nazarin majalisa.

Wannan koke na baya-bayan nan ya ƙara dagula takun-saka tsakanin Sanata Akpoti-Uduaghan da shugaban majalisar dattawa Akpabio.

Badaƙalar ta samo asali ne a ranar Alhamis ɗin wancan makon da ya gabata ne, inda wani zazzafan rikici ya ɓarke a zauren majalisar dattijai yayin da Natasha Akpoti-Uduaghan ta nuna rashin amincewarta da sauya mata kujerar da Akpabio ya yi.

Tana isa wajen zaman ta tarar an cire mata sunanta aka canza mata kujera, hakan ya sa ta buƙaci a yi mata bayanin abin da ta gani a matsayin wani yunƙuri na rashin gaskiya.

Me ya faru a baya?

Ita dai Sanata Natasha ba a wannan karon ne ta fara zargin fitattun maza da yunƙurin neman lalata da ita ba. A shekara ta 2014 ta zargin Mataimaki Na Musamman ga Shugaba Goodluck Jonathan, wato Reno Omokri, da neman lalata da ita.

A ranar Talata, 12 ga Oktoba, 2021, Natashan ta wallafa a shafinta na Facebook cewa, a ranar 6 ga Mayu, 2014, a ɗakin taro na Uhuru Kenyatta cewa, Omokri ya nemi ya yi lalata da ita.

Sai dai kuma, Omokri ya bayar da sanarwar saka biyan diyyar Dala 50,000 ga duk wanda ya bayar da shaidar hoto ko bidiyo na kasancewar sa a ɗakin taron, inda ya ce, a lokacin ba ya Nijeriya ma kwata-kwata. Sannan daga baya ya wallafa tikitin jirgin British Airways da ya hau zuwa Amurka tare da takardun shaidar tambarin hukumomin shige da fice na Nijeriya da Amurka akan fasfo ɗinsa.

Ya ce, a lokacin maigidansa Shugaba Jonathan ya tura shi Amurka a matsayin jakada na musamman kan ’Yan Matan Chibok da aka sace a lokacin, inda ya wallafa hotunansa da jami’an Amurka.

Bayan da Reno Omokri ya wallafa wannan bayanai ne sai Natasha ta cire saƙonnin da ta wallafa na zargin sa. Daga bisani kuma Omokri ya bayar da sanarwar cewa, an biya shi maƙudan kuɗi a matsayin diyyar ɓata masa suna. Wannan kenan.

To, sai dai kuma shi ma Shugaban Majalisar Dattawa Akpabio ba Sanata Natasha ce kaɗai ta taɓa zargin sa da neman aikata masha da ita ba.

A ranar 13 ga Yuli, 2020, tsohuwar Manajar Darakta ta Hukumar Raya Yankin Neja Delta, Joy Nunieh, ta yi zargin cewa, ta sheƙa wa Akpabio mari sakamakon yunƙurin da ya taɓa yi na neman yin lalata da ita.

Nunieh ta yi wannan zargi ne a gidan talabijin na Arise, inda ta ce, hakan ya faru ne a lokacin da shi Akpabio ya ke riƙe da muƙamin Ministan Neja Delta a gidan saukar baƙinsa da ke Abuja.

Sai dai kuma, kamar yadda ya ƙaryata zargin da Natasha ta yi masa ta hanyar fitar da sanarwar manema labarai ta hannun kakakinsa, haka ita ma Nunieh ya fitar da sanarwar ƙaryata ta a lokacin, amma sai dai ba a ga ya garzaya kotu ba ko kuma ita Nunieh ta dawo ta ƙaryata kanta ba, kamar yadda ta kasance tsakanin Natasha da Omokri.

Yayin da tsohuwar ’yar Majalisar Dattawa, Sanata Florence Ita-Giwa (1999-2023), ta ke tofa albarkacin bakinta kan badaƙalar, cewa ta yi, rauni ne daga gare ta a samu wata sanata mace maza suna neman yin lalata da ita, tana mai cewa, wajibi ne mace ta gane matsayinsu ɗaya da kowanne sanata. Don haka bai dace ta bayar da fuskar da har wani zai nemi yin lalata da ita ba.

Daga dukkan alamu dai lamarin na neman zama na aƊnjuma da Ɗanjummai, amma lokaci ne kaɗai zai tabbatar da haƙiƙanin gaskiyar abubuwan da suka faru.

By ukarofi