Daga ABDULLAHI SANI SULAIMAN
A yanzu ka iya cewa babu wani ɗan masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood da yake faɗa da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ko ya yi gudun hijira, don Kano ta yi masa zafi, saboda yanayi na siyasa.
ƙasa da shekara biyu da zaman shi shugaba a wannan hukuma ta tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya dawo da ruhi tare da mutuncin wannan hukuma ta hanyar motsa ta da aikace-aikace, wanda kunne ke ji wasu ma ido ya kan gani.
Haƙiƙa iya gyaran dokokin wannan hukuma wani abu ne da shi kaɗai ka iya sawa a ce da Abba El-Mustapha ‘WELL-DONE’, domin irin namiji ƙoƙarin da ya yi tare da jajircewar ma’aikatan wannan hukuma dole ne ka jinjina wa salon ahugabancin Abba El-Mustapha na ba wa kowanne sashin hukumar damar yin aikinsa ba tare da katsalandan ba, wanda haka ne ya sa ya yi nasarori, kamar haka cikin shekara biyu:
Sashen ɗab’i (Publication):
Wannan sashe na yin aiki dare da rana, domin kawo ƙarshen masu yaɗa kalman batsa da sunan tallen maganin gargajiya, wanda hakan sayar da ya sa aka riƙa zargin Abba El-Mustapha da cewar wai ya bar dukan jaki yana dukan tanki, wato ya bar saka ido akan harkar ’yan fim yana takura wa masu sayar da maganin.
Shirya gasar marubuta irinta ta farko a Jihar Kano da sunan gwamnati tare da ba wa mutum 50 kyauta waɗanda suka yi bajinta a gasar, domin ƙarfafa rubuce-rubucen adabin Hausa. Sashen Finafinai (Film Production And Deɓelopment):
Wannan Sashe yana ƙoƙarin saka ido sosai ga al’amuran ’yan masana’antar Kannywood, domin tabbatar da ba su kauce wa dokar hukumar ba.
Ya Kuma yi nasarar dakatar da manyan jarumai na tsawon shekaru har biyu tare da ƙwace wa wasu jaruman lasisin gudanar da sana’ar fim na dindindin biyo bayan lafukan da aka tabbatar an same su da su.
Shirya horarwa, wato ‘seminar’ ta musamman har karo biyu ga ’yan masana’antar Kannywood, domin inganta sana’arsu.
Sashen Ayyuka Na Musamman (Special Duties):
Abba El-Mustapha shine mutum na farko da ya ƙirƙiri wannan sashe tare da zaɓo wanda zai lura da shi duba da ƙwazonsa.
Wannan sashe ya ƙirƙiri ayyuka da yawa na cigaban wannan hukuma ciki har da haɗa maulidi irinsa na farko da sunan Gwamnatin Jihar Kano, wanda dukkannin sha’irai suka halarta, domin girmamawa ga Annabi Muhammad (SAW), wanda hakan ya ƙara kawo cigaba sosai da haɗin kai ga sha’iran Jihar Kano.
Sashen Kula Da Kotu Da Jami’an Tsaro:
Abba El-Mustapha ya yi ƙoƙarin ba wa wannan sashe damar yin aiki cikin ƙwarewa. Haka ne ma ya sa duk wanda hukumar ta sami irin wannan matsala da shi a gaban kotu ko jami’an tsaro, ba ya zargin hukumar da ci masa zarafi ko bita da ƙulli baya ga yin nasara a dukkannin ayyukan da sashen ya sa a gaba.
Sashen Yaɗa Labarai Da Hulɗa Da Jama’a:
Wannan sashe tun bayan naɗa Abba El-Mustapha a matsayin shugaban wannan hukuma ya ƙara ƙulla alaƙar aiki da wasu manyan-manyan kafafen yaɗa labarai na duniya baya ga na cikin gida. Wannan sashe ya yi nasarar jawo BBC, DW da RFI, wato Radio France, a jiki, domin yin aiki tare. Haka kuma kowa na ganin ayyukan hukumar a irinsu jaridar Sahara Reporters, Arise TV, AIT, NTA baya ga jaridar Daily Trust, Aminiya da DCL Hausa, wanda a yau ba na jin akwai wata hukuma a Jihar Kano da ta ke da alaƙar aiki kai tsaye da irin waɗannan kafafen yaɗa labaran manya baya ga sauran na cikin gida, waɗanda muke jinjina a gare su kullum duba da irin ƙoƙarinsu na yaɗa ayyukan wannan hukuma.
Wannan tsinkaye ne daga Sashen Yaɗa Labarai na Hukumar Tace Finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Sani Sulaiman
