A karon farko gwamnan Ribas ya shigo cikin jama’a tun bayan dakatar da shi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Lahadi ne aka ga Gwamna Siminalayi Fubara da aka dakatar cikin jama’a tun bayan sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas.

Fubara, wanda aka dakatar na tsawon watanni shida a ranar Talata, an gan shi ne sanye da farin kaya.

Hakan ya biyo bayan fitowarsa ne zuwa coci domin yin addu’o’i na addininsa na Kiristanci da aka saba yi, inda ya halarta tare da wasu makusantansa.

A ranar Talata ne Shugaba Bola Tinubu ya sanar da sanya dokar ta-ɓaci a jihar bayan samuwar rikicin siyasa da ka iya haifar da tsaiko ga zaman lafiyar al’umma, wanda hakan ya sa aka dakatar da shi da mataimakiyarsa da ƴan Majalisar Dokoki.

Daga nan ne Shugaban ƙasar ya naɗa Ibok-Ete Ibas a matsayin wanda zai jagoranci harkokin shugabanci a jihar.

Lamarin da ya haifar da cecekuce acikin masu-ruwa-da-tsaki game da harkokin siyasa da ƙungiyoyi masu zaman kansu.

By Babaji