Yadda kotu ta haramta dakatar da ‘yan majalisa ba bisa doka ba a Nijeriya 

Spread the love

Daga FEMI FALANA, SAN

A shekara ta 2010 kamfaninmu na shari’a ya wakilci shari’ar Dino melaye da ‘yan majalisa guda 10 waxanda aka dakatar, sakamakon tuhumar majalisar tarayya a ƙarƙashin mulkin Dimeji Bankole akan hannu cikin rashawa. 

Babar kotun qasa ta dakatar da waxannan ‘yan majalisa ta hanyar ayyana hukuncin a matsayin haramtaciyyar doka kuma ba bisa tsarin kundin qasa ba, sannan ta umurci biyan kuxaxen albashinsu da alawus da aka riqe lokacin dakatawar.

A shekara ta 2012, kamfanin namu ya sake wakiltar shari’ar honourable Rifkatu Danna, wadda ta kasance mace xaya cikin yan majalisan Bauchi 31. An dakatar da Danna a June, 2012 kan zargin ta maida kalamai marasa daxi ga masu zartar da doka a lokacin da ta ke tuhumar hukuncinsu na amincewa na canza muhallin shalkwatar Qaramar Hukumar Tafawa Balewa ta Bauchi. Amma an samu nasarar da Babbar kotun Bauchi ta zartar da hukuncin dakatarwar a matsayin wanda yake haramtacce. Ta kuma bada umarni maida ita aiki tare da mayar mata da kuxaxen albashinta da alawus da aka riqe.

A shekara ta 2017, kotun xaukaka qara ta yi watsi da qarar kukunci Babar kotun Bauchi kan hukuncinta na haramta dakatar da honourable Rifkatu Danna. Kotun ta yi amfani da hujjarmu na cewa dakatar da wannan ‘yar majlisar ya tauye haqqin da kundin qasa ta ba wa yankin Bogoro na ganin cewa an wakilce su a majalisa. Bisa haka kotun ta zartar da hukunci irin na kotun, wato ba ta bi doka ba da ta dakatar da albashi da alawus xinta ba, duba da cewa, ita ba ma’aikaciya ba ce, maimakon haka ta kasance zaɓaɓɓar ‘yar majalisa ce ta garin Bauchi.

A shekara ta 2018, kamfaninmu ya sake wakiltar honourable Abdulmumin Jibrin, xan majalisa wanda aka dakatar tsawon kwana 180, don zargin majalisar tarayya ƙarƙashin mulkin Dogara da ƙari kan kassafin kuxin ƙasa. Babar kotun ƙasa ta hana dakatarwar ta kuma umarci biyan xan majalisar albashi da alawus xinsa.

Babar Kotun ƙasa ta yi watsi da dakatar da Sanata Ali Ndume daga majalisa ƙarƙashin mulkin Bukola Saraki a shekara 2017. Sanatan ya shigar da ƙarar ta hanyar lauyan sa Marcel Oru esq.

Duba da ƙara ta (2017) 49 WRN 82: ƙarar xan majalisar jiha na Bauchi da hourable Rifkatu Danna da ke da kamanceceniya da wannan ya zama hujja da ta yi sanadiyyar nasarar sa. 

Haka zalika, Babar Kotun ƙasa ta zartar da hukuncin dakatar da Sanata Oɓie Omo-Agege a shekara 2020 a matsayin haramtacce da kuma saɓawa doka. Wanda ya shigar da karar a madadin sanatan shi ne lauyansa Edward Omaga Esq.

Wani lokacin a cikin shekarar 2020, majalisar jiha ta Jigawa ta dakatar da xan majalisar su Hon. Sana Isyaku, kan martanin kushe gwamnan jihar Alhaji Muhammad Abubakar Badaru a lokacin da ya ziyarci garin Hadeja don bikini aure. Hon.Isyaku ya kai ƙarar dakatar da shi da aka yi a babbar kotun jaha, inda alƙalin mai suna justice Ahmad ya zartar da cewa, hukuncin majalisar bai yi daidai da tsari na 15 doka ta 74 (2)(c) and (3) a, b na kundin tsarin majalisar jaha na shekara 2017, wanda hakan ya sa ya ya bayyana dakatarwar a matsayin haramun a doka, rashin dacewa. Ya kuma umarci da a biya shi alawans xin Shi na stayin watanni uku, wanda adadinsa zai kai milyan uku.

A ranar 18 ga watan Nuwamba shekara ta 2020 kotun xaukaka ƙara ta yi watsi da ƙorafin dakatar da hukuncin da majalisar jiha ta shigar dangane da hukuncin da Babbar Kotun ƙasa ta yanke akan dakatar da ‘yan majalisu uku. Alƙali Folayemi Omoleye ya tuhumi masu xaukaka ƙarar da kawo ƙorafi marar hujja gaban kotun, ya kuma umarci a mayar da ‘yan majalisan bakin aikinsu na kare haƙƙin doka da gaggawa.

A ranar 13 ga watan Agusta, shekara ta 2024 wannan kotun ta mayar da Honourable Iroji Ogundeji a bakin aikinsa na makaimakin majalisar jiha, inda Justices Oyebisi Folayemi Omoleye, Frederick Oziakpono-Oho, da Yusuf Alhaji Bashir suka aminta da hukuncin Justice Akintan Osadebey, na mayar da xan majalisar mai zama na biyu bisa aikinsa na waƙiltar yankin Odibo.

A cikin shekaru biyar da suka wuce, Babar Kotu da ke zamanta a Lokoja, Jihar Kogi da kotun ma’aikata ta ƙasa sun yi watsi da dakatar da ‘yan majalisar jiha na Jihar Kogi da Edo.

A watan Maris na shekara ta 2024, majalisar wakilai a ƙarƙashin mulkin Akpabio ta dakatar da Sanata Abdul Ningi (xan Jam’iyyar PDP daga Bauchi) tsawon watanni uku kan furucinsa na cewa, an yi wa kasafin kuxin kasa na 2024 ƙari.

Duba da hujjoji da manyan kotu da kotun xaukaka ƙara da dama suka bayar kan haramci da ƙarancin ƙa’idojin dakatar da zaɓaɓɓen xan majalisar ƙasa; dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan babban ganganci ne ga kundin tsarin doka. 

Ya kamata a gaggauta xage haramtaccen dakatarwar, duba da cewa Babbar Kotun ƙasa ta hana komitin sanatoci zartar da kowane irin hukunci har sai ta gayyaci waxanda ƙarar ka shafa, don ba su damar jin ta bakinsu tare da sauraron hujjojinsu. Don haka ya fi dacewa a ce sanatocin sun bi umurnin kotu ta hanyar dakatar da duk wani hukunci don ba wa doka damar yin abinda ya dace.

Daga ƙarshe, hukuncin dakaratar da ‘yan majalisa bisa son rai a matakin jiha da tarayya ba abu ne da ya kamata a bari ya ci gaba a ƙasar nan ba.

Falana babban ƙwararren lauyan lare haƙƙin bil adama ne a Nijeriya

By ukarofi