Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Masarautar Zazzau ta fitar da bayyani bisa shirye-shiryen bukkukuwan Sallah ƙarama na bana kamar haka:
Ranar Sallar Idi: Sakamakon ayyukan gina hanyoyi wanda ke gudana a halin yanzu, saboda cinkoson jama’a da ababen hawa, dukkanin hanyoyin da suka shafi filin Idin Malam Musa kan hanyar Jos, kasancewar za a gabatar da Sallan Idin bana da misalin ƙarfe 8:30 na safe, ta ɓangaren ƙofar Doka da Banzazzau da hanyar Dakace zuwa da dawowa duk za su kasance a rufe ga ababen hawa (motoci da Keke NAPEP da mashina), da zarar an kamalla Sallan Idi, hanyan da ta tashi daga masallacin Idin zuwa ƙofar Doka ta nufi Lemo da Mangwaron Babajo zuwa Rimin Kwa-kwa da kuma Babban Dodo zuwa ƙofar Fadan Maimartaba Sarkin Zazzau duk za su kasance ba tare da ababen hawa ba, sai dawaki da mahayansu.
Rana ta biyu (Hawan Bariki): A sakamakon ayyukan gina sabbin hanyoyi da magudanar ruwa waɗanda suka ratsa dukkanin hanyoyin da ake bi zuwa Hawan Bariki, domin sauƙaƙe wahala ga mahaya da dawakansu, Majalisar Masarautar Zazzau bana ta soke gudanar da wannan Hawa na Bariki har sai in Allah Ya kaimu baɗi.
Rana ta uku (Hawan Daushe): Bayan kamalla gaisuwan Barka da Sallah wanda za a gabatar a Fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau da ƙarfe 9:00 na safiya. Tun daga ƙarfe ɗaya na rana (1:00am), hanyar da ta tashi daga Fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau wanda ta nufi Albarkawa da ƙaura zuwa ƙofar Gayan da Sabuwar Hanyan Azarar Dabuwa zuwa ƙofar Gidan Bellon Gima da Kasuwar Zariya zuwa Kanfage da Babban Dodo zuwa Fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau za su kasance a rufe ga masu ababen hawa sai mahaya da dawakinsu.
Majalisar Masarautar Zazzau tana kira ga masu zuwa Sallan Idi a Dambo da Nagoyi da Dakace waɗanda suke tashi daga cikin gari da su yi amfani da hanyoyin da suka ratsa unguwannin Nagoyi ta ɓangaren cikin gari ko ta tsohuwar hanyar Jos ta gaban FCE ga al’umman da suke fitowa daga ɓangaren Tudun Wada da Gyallesu.
Har ila yau, Majalisar Masarautar Zazzau tana kira ga magidanta masu ajiye ababen hawansu ko gudanar da kasuwanci a gefen titi da su ɗauke ko su ƙaurace wa hanyoyin na tsawon waɗannan kwanaki.
Ga masu kallon hawan Sallah a dukkanin waɗannan kwanakin, masarautar ta buƙace su da su tsaya gefe-da-gefen hanya, ba tare da tsallakawa ko shiga cikin tsakiyar hanyan da dawaki suke bi ba.
Majalisar Masarautar Zazzau na kira ga Jama’a da su bi sauran hanyoyin cikin gari domin gudanar da harkokinsu waɗanda za su kasance a buɗe a tsawon waɗannan kwanaki.
Majalisar Masarautar Zazzau tana godiya da goyon bayan da jama’a suke bayarwa a kowane lokaci, tana ƙara kiran da a ci gaba da ba jami’an tsaeo haɗin kai da goyon baya.
Da fatan za a gudanar da bukukuwan Sallah lafiya.
