Daga HABU DAN SARKI
Kungiyar Marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani, Arewa Media Writers, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamred Haidar H. Hasheem, ta gudanar da taron tattaunawa da uban ƙungiyar na ƙasa (Patron I) kuma shugaban Kwamitin Amintattu na Gamayyar ƙungiyoyin Mutanen Arewa (Coalition of Northern Groups – CNG), Dr. Nastura Ashir Sharif, a cikin ƙwaryar Birnin Katsina.
Da yake jawabi, Shugaban ƙungiyar Arewa Media Writers, na ƙasa Kwamred Haidar H. Hasheem, ya yi gamsasshen bayani ga Dr. Nastura Ashir Sharif, tare da sauran mahalarta taron, inda ya bayyana manufar taron da kuma yadda haɗin gwiwa da CNG zai taimaka wajen gina sabuwar alaƙa mai amfani ga al’umma.
Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai wajen inganta ayyukan ƙungiyar da samar da sabbin dabaru don tallafa wa al’umma, musamman ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta wajen wayar da kan jama’a.
Haka zalika, Dr. Nastura Ashir Sharif, a matsayinsa na babban jigo a ƙungiyar, ya yaba da ƙoƙarin da Arewa Media Writers ke yi tare da ƙarfafa gwiwar shugabannin ƙungiyar na ƙasa da na Jihar Katsina akan muhimmancin amfani da kafafen sada zumunta don wayar da kan matasa da kuma inganta amfani da su yadda ya kamata.
A yayin ziyarar, Dr. Nastura Ashir Sharif, ya bayar da gudunmawar naira dubu ɗari biyar (N500,000) ga ƙungiyar Arewa Media Writers reshen Jihar Katsina, don tallafa musu wajen gudanar da ayyukan da ƙungiyar ta sa a gaba.
Shi ma, Shugaban ƙungiyar Arewa Media Writers na Jihar Katsina, Kwamred Nura Siniya, ya gabatar da jawabin godiya, inda ya godewa Dr. Nastura Ashir bisa gudunmawa da goyon bayan da yake bai wa ƙungiyar Arewa Media Writers wanda ya kasance jagora mai muhimmanci wajen tallafa wa ƙungiyar tun daga lokacin da aka kafata, kawo yanzu.
An gudanar da taron a babban ɗakin taro na Jamvaly Hotel da ke ƙwaryar birnin Katsina, domin tattauna hanyoyin haɗin gwiwa da ƙarfafa alaƙa tsakanin Arewa Media Writers da CNG, da nufin samar da cigaba a fafutikar da ƙungiyoyin ke yi na kare martabar yankin Arewacin Nijeriya.
Taron ya kasance mai matuƙar muhimmanci wajen tsara hanyoyin inganta alaƙa da inganta tsaro a yankin Arewa, da kuma yi wa al’umma jagoranci ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta don wayar da kan matasa akan kyawawan ɗabi’u.
Daga ƙarshe Alhaji Dr. Nastura Ashir Shariff, ya bai wa shugabanni da membobin ƙungiyar Arewa Media Writers shawarwari masu kyau domin ci gaba da tafiyar da ayyukan ƙungiyar cikin tsari domin samun nasara.
