Rikicin cikin gida: Yadda jam’iyyun adawa suka rasa kataɓus

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Batun sauyin sheƙar ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyya mai mulki ya haifar da muhawara kan gaskiyar da ƙimar jam’iyyun. Kusan shekaru biyu kenan tun bayan zaɓen 2023, jam’iyyar APC ta kasance ko dai ta kutsa ko ta mamaye jam’iyyun adawa.

Masu rajin kare haƙƙin ɗan adam da masu nazarin al’amura sun ce, rashin wata jam’iyyar adawa mai ƙarfi ya haifar da rauni ga dimukraɗiyyar Nijeriya, domin bibiyar ɓangaren zartarwa ya jawo ƙarancin bayanai game da ayyukan gwamnati.

A kwanakin baya ne gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ɗan jam’iyyar adawa ta PD, wanda ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga zarcewar Shugaban ƙasa Bola Tinubu a 2027.

Cikin shaguɓe Mista Eno ya nuna cewa yana gab da sauka daga jirgin da ke da matsala zuwa wani jirgin daban.

Kafin waɗannan kalamai, gwamnan jihar Delta, Sheriff Oboreɓwori, ya sauya sheƙa tare da dukkan ‘yan jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a ƙarshen watan Afrilu wanda hakan ya sauya matsayin jam’iyyar adawa a yankin Kudu maso Kudu mai arziƙin man fetur wacce ta shafe shekaru 26. Akwai kuma rahotanni da ke nuna cewa sauran gwamnonin PDP na gab da ɗaukar irin wannan mataki.

Mista Oborevwori shi ne ya gaji, Ifeanyi Okowa wanda ya yi wa Atiku Abubakar takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2023, tare da ƙarin dandazon mutane.

Mista Oborevwori ya ce, dalilin komawa jam’iyyar APC shi ne irin ƙaunar da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya nuna wa jihar Delta. Na yi imanin cewa ƙaunar da fadar ke nuna wa jihar na buƙatar samun goyon bayan jihar a zaɓen 2027.

“Wannan yunƙuri ba za a kira shi da sauyin sheƙa ba, mu (gwamnoni) mun yarda kan za mu ne gabaɗaya kuma idan mun koma, za mu samu damar cin mariyar abin da ke can sama,” ya faɗa.

Wannan kalamai nasa sun haifar da zarge-zarge kan yunƙurin samun ƙarin ‘yan jam’iyyun adawa da ka iya komawa jam’iyya mai mulki.

Ko da a majalisun tarayya, an samu wasu da dama da suka yada jamiyyunsu suka koma jam’iyya mai mulki ta APC.

Wasu ƙungiyoyi masu rajin kare haƙƙin bil’adama sun ce wannan guguwa ta sauyin sheƙa na ƙara tabbatar da yunƙurin samar da ƙasa mai jam’iyya ɗaya da kuma mulkin kama-karya ne.

ƙungiyar ta ce, “wannan ni lissafi ne da dabara” da gwamnatin shugaba Tinubu ke yi domin tarwatsa ginshiƙin dimokraɗiyya na ƙasar nan zuwa ƙasa mai jam’iyya ɗaya ta hanyar ba da cin hanci da zarge-zarge ko tilastawa.”

Sai dai fadar shugaban ƙasa ta yi wastsi da zargin da cewa babu ko tushe balle makama,”

Kawunan jam’iyyun adawa dai a rabe suke kuma ba su da tasiri, kuma haka abin yake ga jam’iyyar PDP da LP waɗanda ke cikin tsaka mai wuya wanda ya bai wa APC damar yin nasarar a zaɓen shugaban ƙasa a 2023. Ga kuma jam’iyyar NNPP ita ma da ta shiga layin irin wancan hali na sauran jam’iyyun adawa.

Rikicin iko da a jam’iyyun adawar Najeriya ya jawo sun tsattsage gida biyu inda shugabancinsu ya zama a kullum ƙoƙari yake ya ga yadda za su rayu a maimakon sako jam’iyya mai mulki a gaba ta hanyar suka mai ma’ana da kawo tsare-tsare da suka saƙa da na gwamnati.

Jam’iyyar PDP, wacce ta taƙa zama mafi girma da mamaya, a yanzu tana fama da rikici da cin dunduniya da rashin kyakkyawan shugabanci. A ƙarƙashin muƙaddashin shugaban jam’iyyar, Umar Damagum, jam’iyyar tana fama da rikici kuma da yawa har a sauran rassan jam’iyyar saboda rashin haɗin kai. ɗaya daga cikin jigo a jam’iyyar shi ne Nyesom Wike, tsohon gwamnan Rivers wanda ke aiki a ƙarƙashin gwamnatin APC mai mulkin ƙasa. Sauran tsagin jam’iyyar kuma na mara wa Atiku Abubakar baya wanda ya yi mata takarar shugaban ƙasa a 2023. Ga kuma tsagin gwamnan Bauchi Bala Mohammed.

Wasu daga cikin masu fashin baƙi sun bayyana PDP a matsayin wata ƙanwa ce ga APC saboda gaza taƙuka abin a-zo-a-gani wajen ƙalubalantar tsare-tsaren gwamnati.

A lokacin da Ned Nwoko, sanata mai wakiltar Delta ta Arewa ya koma APC a watan Janairu, ya bayyana PDP da jam’iyya mai fama da “zuzzurfan rarrabuwar kai da rikicin cikin gida” a mataki na jiha da ƙasa a yayin da yake tunanin barin jam’iyyar.

Jam’iyyar LP wacce ta samu gagarumin goyon baya daga matasa da masu zaɓe a birane ita ma na fama da rikicin cikin gida da matsalolin shari’a da na karƙe iko.

Haka kuma, jam’iyyar NNPP ta sha irin nata rikon cikin gidan a Kano wadda ita ce jihar da take da gwamna a Najeriya. Kawu Sumaila, sanata mai wakilta Kano ta kudu, ya bar jam’iyyar, ya koma APC. Sannan ana sa ran ƙarin wasu ‘yan majalisar da za su fice a nan gaba.

Masu nazari na ganin cewa, rashin kyakkyawar tsari da mara wa ‘yan siyasa baya, ya jawo raunin shiga ga jam’iyyu, kuma ya sa jam’yyun sun yi rauni wanda ya sa zai yi wahala haɗa kan jam’iyyun adawa.

Ana zargin APC da amfani da arziƙin ƙasa wajen gwara kan shugabannin jam”iyyun adawa ko tilasta musu, sai dai zargi ne da jam’iyya mai mulki ta sha musantawa.

“Ana zargin dai akwai wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyun adawa da aka saye su wanda ya jawo rashin yarda a tsakaninsu,” a cewar mai nazarin jam’iyyun siyasa, Dakuku Peterside.

“Idan ya zama ana zargin akwai wani jigo ko wasu da aka saye, wannan na jawo babbar matsala a jam’iyyar.

“Jam’iyyun adawa an riga an yi musu rauni ta hanyar barin APC ta gudanar da yyukanta ba tare da wasu da ke kawo tasu fahimtar ba. Tamkar duk APC ta mai da su rassanta. Kuma rashin haɗin kai ya ƙara bai wa APC damar muƙe ƙafa ta gudanar da sha’aninta ka har da kokarin mai da ƙasar mai jam’iyya ɗaya.”

Haka kuma, ta fuskar tursasawa, APC na maimaita abin da PDP ta yi ne a shekarar 1999, inda PDP ta lashe zaɓen shugaban ƙasa da kujeru 241 cikin 360 na ‘yan majalisar wakilai da kujeru 71 cikin 109 na ‘yan majalisar datttawa da gwamnoni 21 cikin 36 da ake da su a Najeriya.

Bayan shekaru 4 aka rika samun ‘yan jam’iyyar adawa da ke dake tururuwar komawa PDP domin su samu kaso su na arziƙin ƙasa. PDP ta lashe kujeru 28 cikin 36 na gwamnoni da samun kujeru 76 na kujerun sanatoci. Yanzu kuma reshe ya juye da mujiya ne. Ba ta da tabbacin nawa ne cikin gwamnoni 11 da ta samu a zaɓen 2023 za su rage a jam’iyyar.

Mista Peterside ya ce, jam’iyyun adawa sun gaza wajen kawo tsare-tsare na daban a yayin da suke barin gwamnati ba tare da fuskantar kowanne irin tirjiya ba da kuma nema wa al’umma biyan buƙatunsu.

“Adawa mai ma’ana na zama mai sa ido ce ga ayyukan jam’iyya mai mulki a yayin da take ƙoƙarin samar da tsare-tsaren na daban domin bunƙasa shugabanci.”

“Idan aka ce babu wata muhawara kan tsare-tsaren na ƙasa, ana yanke abubuwa da a wasu lokuta ke buƙatar nazari daga al’umma. Ga misali, a lokacin da shugaba Tinubu ya cire tallafi mai a 2023, jam’iyyun adawa sun gaza kawo wata hanya da za a magance matsalar, inda suka bar ƙungiyoyin al’umma suna gudanar da zanga-zanga a kan tsadar rayuwa,” a cewar Mista Peterside.

By ukarofi