A Nijeriya ne kawai, kuma a Arewa, nama da abinci ya zama wani kayan gabas, amma ko a Nijar nama ba wani abin da za a zo ana an ci ya yi yawa ba ne. Hatta a irinsu Cotonou da Togo da Burkina Faso.
’Yan Nijeriya sun saba cin wake da shinkafa da mai da yaji ko ɗan wake. Shi ya sa ko a manyan gidajen jaridu idan suna hira ko da da manyan ‘celebrity’ ne irinsu Ali Nuhu ko Rahma Sadau da sauransu idan aka tambaye su mene ‘faɓourite food’ ɗinsu sai su ce wake da shinkafa da mai da yaji.
Sama da ahekara 100 wannan abincin da ake bayarwa. Shine dai abincin da ake ba wa alhazai, kuma duk jihar da ka leƙa masaukinsu babu wanda ya fi na wani. Shinkafa ce da kaza ko nama ko kifi. Da safe kuma ƙwai da dankali da biredi da madara, sai ayaba da tuffa da ake bayarwa.
A bara ne kaɗai alhazai suka sha wahala, musamman na Kano, aka ba su gabza. Da safe har koko da ƙosai ko kunu an ba su. An ba su fanke guda biyu, an ba su wake da shinkafa da tuwo miyar kuka.
Amma duk sauran shekaru sama da 10 haka abincin alhazai yake, haka masaukin alhazai yake. Ni wallahi ma da yake da kuɗina na biya na je, hatta ɗaki sai da na zaɓa. Na kuma ce ga adadin mutanen da zan iya zama da su. Ba zan iya zama a ɗaki mu biyar zuwa shida ba. Hatta umrah idan na je haka nake cewa masu masauki, ba zan iya zama mu wuce mu uku ba. Sai an roƙe ni nake yarda mu zauna a ɗaki mu huɗu.
Idan na ji ku na maganar nama, wallahi haushi da kunya na ke ji. Saudiyya ba garin da nama ya zama wani abu ba ne. Wallahi wannan azumin da na je umrah ni daina cin naman na yi da ya ginshe ni. Na daina shan Lábban Mara’i da ta ginshe ni. Zamzam ne kawai bai ginshe ni ba. Amma ruwa ma da ake ba mu sai dai na wanke hannu da shi. Dabino kuwa wallahi sai da na daina karɓa a harami, don na daina cin sa, ya daina ba ni sha’awa ko ɗanɗano. Lemon kwali kuwa sai dai na tara na bar shi.
Akwai wani abokina da ya ba ni dambum kaza da ya zo da shi daga Nijeriya da samosa wallahi ko ɗanɗanawa ban yi ba. A firjin ɗakinmu na bar shi. Idan ka ga firjin ɗakinmu cike da kayan alatu, su tuffa da ayaba da lemo. Wasu ma duk Sabil ne ake ba mu ko a harami ko a hanya. Har su ‘ice cream’ ba mu ake. Sannan akwai mazauna can masu kawo min ziyara suna kawo kayan sannu da zuwa.
Wallahi haushi na ke ji na ji ana maganar nama zuƙu-zuƙu a Saudiyya. Sun saba a Nijeriya da yanka biyu-uku ƙanana, kaza sai an yi wata ko sama da haka za a ci. Ko idan an saya ta Yahuza a ɓuya a ci ana ganin kamar wani ƙurewar daɗi ne. Kuma fa da kuɗinsu suka biya suka je aikin hajjin ba za su ga yawan naman da ake ba su ba tunda zai shiga cikin lissafin Naira miliyan 8.5 ɗin. Kuma ko umrah ka je Saudiyya nama sai ka ture, sai ka ji ka daina sha’awarsa. Nama har a bola wallahi ga shi nan. Ko lokacin da na je aikin hajjin 2016 abin da ake ba mu ya fi wannan ma, lokacin duniya na kwance tana barci kenan. Mu abincin ma har da na rana wallahi, haka suke ajiye mana. Idan ka dawo za ka tarar da na rana, ga na dare ma.
Akwai wata mata da ba zan manta da ita ba. Irin mutanen ƙauye ce da aka biyawa. Ina jin cikin waɗanda A.A Rano ya biyawa ce. Ta dinga wanke naman da ake ba ta tana shanyawa a ɗakinsu. Ta ɗauki na mutane ma ta wanke ta shanya, ta ce, idan ya dawo Nijeriya sa dafa su ci da ‘ya’yanta. Wallahi buhu guda ta yi bayan kilonta 43 kg. Da muka zo Jiddah an sha dariya. ƙarshe masu jirgin suka yi mata alfarma suka tausaya mata suka auna mata shi ‘free’, saboda abin dariya da tausayin da ta ba su.
Gaskiya a duk abinda kuke faɗa na gaji da jin maganar nama. Duk ‘deɓeloped country’ nama ba matsalarsu ba ce. Ku shiga gidajen da aka sauke mutanen wata jihar, za ku ga su ma naman wasu ma ya fi naku. Ku leƙa otel ɗin mutanen Lagos su da suka saba da cin nama, za ku sha mamakin nama. ƙila ma su da safe akwai farfesun kaji ko na ganda ko naman da ake haɗa musu da shi a karin kumallo.
Ni ɗan Kwankwasiyya ne kuma masoyin Kwankwaso da Abba Gida-Gida, amma wallahi na gaji da jin maganar nama a Saudiyya. ƙauyanci ne gaskiya. A kurkukun Saudiyya ma nama sai ka ci ka ture!
Malam Larabi marubuci ne kuma ɗan siyasar Kwankwasiyya a Jihar Kano. Za a iya samun sa a 08065418892
