Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Hukumar Kula Da Guraren Hada-hadar Fetur Da Gas Babu Haraji ta Nijeriya (OGFZA), Bamanga Usman Jada, ya bayyana Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin alheri ga Nijeriya, domin ƙasar na samun nasarorin da ba a taɓa samun irin su ba a ɓangarori da dama na tattalin arziki ƙarƙashin jagorancin sa.
Jada ya faɗi haka ne a lokacin da ya samu wasiƙar yabo ta Mafi Kyawun Shugaban Hukuma da Jaridar Blueprint ta ba shi gabanin bikin bada lambar yabo da za a gudanarwa a ranar 22 ga Yuli, 2025.
Ya ce, hukumar OGFZA ta jawo jarin dala biliyan 24 da kuma alƙawarin zuba jarin dala biliyan 30 a ƙarƙashin jagorancin shugaba Tinubu.
“Ina son in bayyana yadda mu a matsayinmu na hukumar gwamnatin tarayya, muka himmatu wajen tallafa wa ajandar Renewed Hope na shugaban ƙasa, aikinmu shi ne tsarawa, gudanarwa, sa ido da ba da izini da lasisi ga duk masu zuba jari a fannin mai da iskar gas na wannan ƙasa. Wani ɓangare na babban nauyin da ke kanmu shi ne jawo hankalin ‘yan waje wajen saka hannun jari na cikin gida.
“Tun da aka kafa wannan gwamnati, mun shaida irin alƙawurran da aka ɗauka na zuba jari daga ƙasashen waje da kuma na cikin gida, masu zuba jari suna da kwarin gwiwa kan shugabanci da hangen nesa na shugaban ƙasa, suna ganin sadaukarwar da ya yi na samar da yanayi mai kyau na kasuwanci, a sakamakon haka, mun samu nasarar jawo jari da dama, waɗanda a yanzu muke bin diddigin su don tabbatar da an samu ci gaba.
“Misali, ba da daɗewa ba, mun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tare da wani kamfani na ƙasar Sin da abokan hulɗar ƙasar Jamus don samar da wani tsari na zamani a shiyyarmu ta Akwa Ibom don samar da makamashi mai ɗorewa,” inji Jada.
Jada ya kuma yaba wa mahukuntan Kamfanin Jaridun Blueprint bisa wannan karramawar, inda ya ce ba zai ɗauki hakan a matsayin abin wasa ba.
“Abin da nake so in ce shi ne na gode, na gode sosai ga jaridar Blueprint da ku ka karɓe ni, ina matuƙar godiya da goyon bayan da ku ke badawa, kuma ina yaba muku da jajircewarku na tabbatar da ɗa’a, gaskiya da riƙon amana.
“Jaridar Blueprint ta zama sananniya a ƙasar nan, kuma kowa ya san irin kyakkyawan ayyuka da ku ke yi, muna godiya da yadda ku ka goyi bayan naɗin da aka yi wa Ministan Yaɗa Labarai wanda ya fito daga wannan kamfani mai martaba, mai riƙon amana. Ba mu da kalmar godiya gare ku.
“Ayyukan da ku ke gani ba nawa ba ne kawai, sun samo asali ne daga ƙwazo a cikin hukumarmu, a nan tare da ni akwai babban manajan mu mai kula da harkokin kuɗi, da babban manajan sayar da kayayyaki, da kuma SA ga MD a kan sayen kayayyaki. Tsayuwarsu da jajircewarsu ta sa waɗannan nasarorin suka samu.
“Ina alfahari da cewa wannan karramawa ta fito ne daga jaridar Blueprint, wata kamfani da ta shahara wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana, na sake gode muku bisa yadda muka amince da ƙoƙarinmu.
