Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A ƙoƙarin ta na mai da tubabbun yan ta’adda cikin al’umma, gwamnatin Jihar Katsina ta shirya buɗe ajijuwa na koya masu karatun yaƙi da jahilci.
Za a buɗe ajijuwan ne a ƙananan hukumomin da ‘yan ta’addan suka ajiye makamin su tare da rungumar sansaci.
Babban daraktan ilimin ya’ya mata da yaƙi da jahilci, Hajiya Bilkisu Muhammad Kaikai ta faɗi haka a wata hira da manema labarai a ofishin ta da ke Katsina.
Ta ce hukumar za ta koyar da darussan addinin Musulunci da karatun boko domin canza masu rayuwa da halayen su da zai daidaita da na al’ummar yankunan su.
Hajiya Kaikai ta bayyana cewa hukumar ta za ta haɗa kai da ƙananan hukumomin da shirin ya shafa domin ganin an samar da ajijuwan.
A cewar ta cikin watanni shida hukumar ta buɗe irin waɗannan ajijuwa guda 68 a faɗin jihar.
Haka kuma hukumar ta za ta fara gudanar da darussa wa ‘yan gidan gyaran hali waɗanda basu kammala karatun digiri ba aka kai gidan.
Hajiya Bilkisu Kaikai ta bayyana cewa ta fara rangadin ƙananan hukumomi a jihar domin gani da ido halin da azuzzuwan yaƙi da jahilci da cibiyoyin mata ke ciki.
Daga nan sai ta yabawa gwamna Dikko Raɗɗa kan irin goyon baya da yake baiwa shirye shiryen hukumar.
Shugaban hukumar ta kuma yi kira ga ‘yan majalisar tarayya da yan majalisar jihar da su ware wani kaso na kuɗaɗen aikin mazaɓar su domin su gina irin waɗannan azuzzuwa da cibiyoyin mata a mazaɓar su.
