Jirgin ƙasa: Dalilin Nijeriya na haɗa ƙasar da Jamhuriyar Nijar

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC), Kayode Opeifa, ya ce aikin hanyar dogo daga Kano zuwa Maradi na da muhimmanci wajen inganta samar da abinci a Nijeriya.

Opeifa, wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar a gidan talbijin na Channel, ya ce layin dogo tsakanin Nijeriya da jamhuriyar Nijar na da matuƙar muhimmanci domin hakan ne mafitar samar da wadataccen abinci.

“A bisa ga AU 2063, ƙasashen Afirka suna ƙarfafa alaƙa da ƙasashen da ba su da ruwa, saboda akwai damar da za a samu a waɗannan ƙasashe, ta hanyar samar da abinci ga Nijeriya da Afirka ta Yamma a ɓangaren hatsi da kiwo wanda ke da nasaba da Maradi. Don haka, za ku iya ganin dalilin da ya danganta Kano da Maradi.

Ya ƙara da cewa, “layin dogon yana tsakiyar cibiyar samar da abinci, kuma shi ne abin da Kano-Maradi, wanda zai zama Kano zuwa Kaduna, Kaduna zuwa Abuja, Abuja zuwa Legas, zai wakilta.”

Opeifa, ya ce gwamnati ta himmatu wajen ganin an haɗe manyan biranen ƙasar ta hanyar sabon taswirar layin dogo.

Ya ce akwai shirye-shiryen gwamnatin tarayya na ɓullo da sabbin layin dogo a cikin birane.

Sai dai ya ce tsarin layin dogo da aka koma cikin jerin gwanon lokaci guda, ya samar da damammaki ga jihohi su samu tallafi don bunƙasa layin dogo.

A yanzu gwamnati ta yanke shawarar yin sabon taswirar kayayyakin more rayuwa na layin dogo, kuma don tabbatar da an haɗe manyan biranen ƙasar,” inji shi.

Shugaban NRC ya kuma ce mazauna yankin na da hannu wajen kare ababen more rayuwa na dogo.

Ya ce, “Yanzu haka, gwamnati ma tana bin Kano-Maradi, mutane da yawa ba su fahimci mene ne ainihin hakan ba, abin da suke ji shi ne Maradi.”

By ukarofi