‘
Daga HABU ƊAN SARKI a Jos
Kwamishinan ýan sanda na Jihar Filato, Emmanuel Olugbemiga Adesina ya tabbatar da kama mutane 22 da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa wasu matafiya 12 da suka fito daga Zariya a Jihar Kaduna, kan hanyarsu ta zuwa biki a Ƙaramar Hukumar Qua’an-Pan ta Jihar Filato.
Ya kuma ƙara da cewa, an kuɓutar da mutane 14 waɗanda babu abin da ya same su, yayin da wasu 21 ke samun kulawar likitoci a babban asibitin Mangu.
A wani labarin kuma, ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam ta Jihar Filato ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa waɗannan matafiya, da basu ji ba basu gani ba. Tare da kira ga al’ummar musulmi na jihar su yi haƙuri, kada kowa ya ɗauki doka a hannun sa, yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin ɗaukar matakin da ya dace.
A wani taron manema labarai da ƙungiyar ta kira, ta bakin Sakataren ƙungiyar na Jihar Filato, Dr Salim Musa Umar, ya yabawa Gwamnan jihar Caleb Mutfwang, saboda gaggawar ɗaukar mataki tare da ziyartar wurin da abin ya faru. A cewar ƙungiyar, “Lallai gwamna ya nuna kyakkyawan shugabanci da damuwa game da abin da ya faru, wanda hakan ya faranta ran mu sosai.”
JNI ta kuma nemi gwamnati da jami’an tsaro su gaggauta gano waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki, don a hukunta su. Sannan kuma, gwamnati ta biya dukkan waɗanda abin ya rutsa da su diyya, kuma a ƙara tsaro a hanyoyin jihar.
Ita ma ƙungiyar matasan Musulmi ta NACOMYO ta nuna ɓacin ranta da kisan wulaƙancin da aka yi wa matafiya a cikin Jihar Filato, tare da ƙara yin kira ga gwamnatin jihar ta tabbatar ta kawo ƙarshen kashe-kashen rayukan da ba su ji ba ba su gani ba, da suka haɗa da mata da ƙananan yara, a ƙauyuka da hanyoyin jihar.
A cikin wata takarda da ƙungiyar ta raba wa manema labarai a Jos, mai ɗauke da sa hannun Shugaban Ƙungiyar na ƙasa Malam Sani Suleiman Maigoro, an yi kira ga matasan Musulmi su kai zuciya nesa, kuma su guji ɗaukar doka a hannu, don hana cigaba da zubar da jini da asarar rayuka.
A yayin haɗa wannan rahoto haɗin gwiwar jami’an tsaro na sojoji da ýansanda na sintiri a cikin garin Jos, don hana ɓarkewar wani tashin hankali da sunan ɗaukar fansa.
