
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta ce babu barazanar tsaro a birnin tarayya Abuja ga al’umma.
Gwamnatin ta bayyana haka ne a ranar Litinin bayan da hukumomin Amurka a Nijeriya suka gargaɗi baki ɗaya ƴan Amurka da su ƙaurace wa dukkan sansanin sojoji da ofisoshin gwamnati a birnin.
A sanarwar da hukumar US Mission Nigeria ta fitar, ta yi kira ga ma’aikatan ofishinta na jakadanci da iyalansu da su ƙaurace wa wuraren sojoji da gine-ginen gwamnati musamman waɗanda ake gudanar da taruka.
Akan haka ne gwamnatin Nijeriya ta ofishin Ministan Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ce Abuja tana nan da aminci ga ƴan ƙasa, mazauna da ma ƴan ƙasar waje.
Ya ce, hukumomin tsaron Nijeriya suna aiki tuƙuru wajen ganin babban birnin da al’ummar da ke cikinta sun samu tsaro.
Ya kuma ce, suna sane da halin rikicin da ke faruwa a sassan duniya, saidai hakan bai sa jami’an tsaron Nijeriya sun yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaro ga al’umma.
