
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu bayani na sirri sun nuna cewa Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta yi aiken saƙo ga Moses Gara, wanda shi ne Kwamandan Atisayen Whirl Stroke (OPWS) game da wani shiryayyen hari a ƙauyukan Jihohin Benuwai da Nasarawa a watan Mayu.
A shekara 2018 ne Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta ƙaddamar da atisayen, wanda ya ƙunshi jami’an sojoji, ƴan sanda da na DSS.
A ranar 13 ga watan Yuni ne ƴan bindiga suka farmaki al’umma a Ƙauyen Yelwata dake Ƙaramar Hukumar Guma a jihar Benuwai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da guda 200 tare da ɗaiɗaita wasu dubunnai.
A bayanan, an samu batun cewa harin an shirya shi ne da nufin kai ramuwa ga wasu dabbobi da Gwamnatin jihar ta ƙwace daga wasu makiyaya.
Ƙauyukan da aka shirya kai musu hari sune Mararaba, Jangargari, Wurgi, Gidan Antonny, Akon, Usende, Gaar, Vandikya, Chiata, Dooga, Gidan Baban Yara, Apelle, Pantaki, Kaambe d kuma yankin ‘Stadium area’.
Haka kuma, akwai shirin kai wa ƙabilar Tibi hari a ƙauyukan dake iyakokin Nasarawa da Benuwai daga wasu ƴan bindigar Fulani, kamar yadda takardar ta bayyana.
