Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara ta bai wa mata 100 tallafin Kuɗi

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Uwargidan gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bai wa mata 100 tallafin Kuɗi karkashin shirin tallafawa mata na ofishin gwamnan jihar ta Zamfara tare da haɗin gwiwa da ofishin uwargidan gwamnan Hajiya Huriyya Dauda Lawal.

Da take ƙaddamar da rabon tallafin kuɗin da aka gudanar a sakatariyar JB Yakubu ta jihar a Gusau, yau Laraba, uwargidan gwamnan Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bayyana cewa a ƙarƙashin shirin an ware mata 100 da aka zaɓo zuwa kashi biyu inda za a bai wa wasu 300,000 kowaccen su, wasu kuma za su samu N500,000 kowacce mace ɗaya.

A cewarta, karimcin zai kasance mai ɗorewa domin tabbatar da cewa an ɗauki kowa da kowa a cikin mata masu rauni, ƙungiyoyin mata, mata ‘yan siyasa da kuma tsofaffi.

A cewarta, makasudin shirin shi ne a sanya mata cikin ƙananan sana’o’i yayin da suke gidajen aurensu musamman alummar dake yankunan karkara domin samun ci gaban tattalin arzikin su tare da dogaro da kawunan su.

Ta buƙaci waɗanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kuɗaɗen da aka ba su yadda ya kamata domin rayuwar su ta inganta .

Ta ƙara da cewa ofishinta zai ci gaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da na maigidanta watau gwamna Dauda Lawal, domin nemo wasu tsare-tsare da za su inganta rayuwar alummar jihar musamman mata da ƙananan yara masu rauni.

“Zan ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da ofishin mijina a matsayin sa na gwamnan jihar da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki domin ganin an samar da wasu tsare-tsare da za su yi tasiri a rayuwar mata da ƙananan yara a jihar.” Inji Hajiya Huriyya.

By ukarofi