Kusan kullum sai an kashe Falasɗinawa!

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Duk lokacin da mutum ya leƙa halin da a ke ciki a Gaza zai ga labara ne na zubar da jini kuma ba alamun ranar daina yin hakan. Kamar dai mutan Gaza ba ma rai ne a jikin su ba. Kashe Bafalasɗine a Gaza ko ma a sauran yankunan Falasɗinawa irin yammacin Kogin Jodan duk ba wani abu ne sabo ko mai tayar da hankalin duniya ba. ’Yan ƙasashen da ke nuna tausayawar ma sai da baki su ke iya magana ko tura tallafi. In da a ce daf akin ma a na amfani da abun da su ke faɗa da dama-dama. Masu sharhi da na gani musamman a Nijeriya na tunanin yaƙin da Isra’ila ta kai Iran zai kawar da hare-haren Isra’ila kan Gaza. Aƙalla dai yakin ka iya sa Gazawa su ɗan numfasa amma sam ba haka lamarin ya auku ba. Gaskiyar magana tamkar Isra’ila ta ƙara yawan kashe-kashen ne ma. Akwai lokacin da ta auna masu jiran samun abinci ta kashe su ba tausayi don ai Falasɗinawa marar sa daraja a wajen ta. Duk lokacin da Isra’ila ta kai irin wannan mugun hari kan gidaje ko sansanonin gudun hijira ta kan ce yunƙurin murƙushe Hamas ne. Shin duk al’ummar Gaza ‘yan Hamas kuma ‘yan Gaza kakaf na marawa aikin mayaƙan Hamas? A dai yadda Isra’ila ta nuna sai fat a kasha dukkan mutan Gaza miliyan 1.2 sannan hankalin ta zai kwanta kan ta gama da Hamas. Mun tuna a kwanakin baya ma ai shugaban Amurka Trump ya nemi al’ummar Gaza su fice daga yankin su koma kasashen makwabta da sunan amfani da dammar wajen sake gina Gaza. Wannan dai bai samu karbuwa a wajen Falasɗinawa ba don kai tsaye sun fassara hakan da yunƙurin raba su da ƙasar su ta gado. Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya so amfani da dammar wajen korar Falasɗinawa don mayar da Gaza tamkar sansanin sojan Isra’ila. Akwai babban yanki ma a Gaza da Isra’ila ta yanka a yanzu ta mayar da shi da’irar tsaro. In ka ɗebe nuna takaici da wasu ƙasashen Larabawa ke yi kan halin da Falasɗinawa ke ciki sai lokacin da a ka samu Afurka ta Kudu ta kai ƙarar Isra’ila Kotun Duniya don tuhumar kisan ƙare dangi kan Falasɗinawa.

Motsi ya fi laɓewa don duk da Kotun Duniya ba za ta samu ƙarfin hukunta shugabannin Isra’ila ba don yadda duniya ta ke ba adalci, aƙalla kotun ta umurci Isra’ila ta dakatar da kisan ƙare dangin nan take da ɗorawa Isra’ila laifi. Netanyahu ya fito ya shashantar da matsayar kotun kuma ba abun da duniya za ta iya yi don duniya ko manyan ƙasashe masu makaman nukiliya na marawa Isra’ila baya. Ita ma Afirka ta Kudu don ta kama ƙasa ne don abun da ta taɓuka ya jawo ma ta bita-da-ƙulli da ma suka daga Jamus. Akasarin ƙasashe na kaffa-kaffa wajen furta matsayar su kan Isra’ila inda su kan zabi cewa a maida zuciya nesa kuma kar a bari yakin ya ƙara faɗi. Duk kamfen ɗin Larabawa na a kafa ƙasar Falasɗinu gefe da Isra’ila ba ya samun karɓuwa a tsakanin magoya bayan Isra’ila. A wajen Isra’ila fa yankin Falasɗinawa ma mallakar ta ne don haka Falasɗinawa na ƙarƙashin mulkin ta kuma tun da su ba Yahudawa ba ne to sun fara tamkar bayi ko waɗanda a ke yi wa mulkin mallaka. Mun san komai na Falasɗinawa sai ya biyo ta hannun Isra’ila kuma hatta ‘yar mashigar nan ta Rafah da ke ƙuryar kudancin Gaza kan iyaka da Masar a rufe ya ke kuma ko an buɗe don shigo da kayan agaji sai Isra’ila ta amince. Duk lokacin da a ka samu shugaban Masar mai sha’awar buɗe mashigar ta Rafah don Falasɗinawa su rika samun tudun mun tsira ko mashigar kayan masarufi to zai yi wuya ya ɗore kan mulki. Ai mun ga abun da ya faru da marigayi shugaban Masar Muhammad Morsi. A Ramallah inda gwamnatin Falasɗinawa ta ke ƙarƙashin Mahmud Abbas baa bun da a ke iya cimmawa sai maganganu da ba lallai su yi tasiri ba. Kuma duk da yadda yankin na yammacin Kogin Jodan ya ke ba turjiya irin ta Hamas a Gaza amma bai hana kasha Falasɗinawa a yankin ba.

Akwai dubban Falasɗinawa da ke kulle a gidajen yarin Isra’ila. Me za mu yi tsammanin zai faru in Hamas ta kwance damarar gwagwarmaya ta miƙa wuya ga Isra’ila? Ni a gani na shikenan batun kafa ƙasar Falasɗinu ya ƙare kuma Isra’ila ta samu dammar ci gaba da bautar da Falasɗinawa da kasha ko ɗaure duk wanda ya daga ma ta yatsa. Sadaukar da rai ga Falasɗinawa tamkar gado ne da su ke yi ala tilas. Yaron da ya yi sa’ar tashi ba a kasha shi ba amma an kasha iyayen sa ba zai zama mai fargaba ga maƙiyi ba. Rayuwar da ba zaman lafiya kullum kuma a kan samu wasu na barci ma a jefa mu su bom a kasha su to ai ta zama rayuwa mai ban takaici da ruɗani. Ta kan kai ga waɗanda a ka kwantar a asibiti ma ba su tsira daga kisa ba kuma in an kashe su ba wani mataki na bin kadun ran su da za a yi in an yi sa’a Isra’ila ta ce ta na bincike kan lamarin ko ta auna ‘yan Hamas ne da dama-dama. A fili fa kamar Isra’ila ta yankewa dukkan Falasɗinawa hukuncin kisa ne inda ta ke zartar da hukuncin ta hanyar kisan ƙare dangi.

MUMMUNAN HARIN ISRA’ILA KAN GAZA YA YI SANADIYYAR MUTUWAR FALASɗINAWA 72

Mummunan harin Isra’ila a kwab ɗaya kuma a dare ɗaya ya yi sanadiyyar mutuwar Falasɗinawa 72.

Wannan fa na zuwa ne daidai lokacin da a ke sabon tsammanin ƙulla sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra’ila.

Yaƙin da zuwa yanzu ya kai wata 21 bai taba saurarawa Falaszinawa don da zarar an samu tsagaita wuta sai wani ƙaramin dalili ya sa Isra’ila komawa ruwan wuta.

A sabon harin an kashe yara uku da iyayen su a sansanin Muwasi da ke daf da garin Khan Younis na kudancin Gaza.

‘Yan uwan yaran sun bayyana cewa an kasha yaran da iyayen yayin da su ke barci.

Kakar yaran mai suna Suad Abu Teima ta nuna matuƙar juyayin kisan gillar da tambayar shin me laifin yaran nan da a ka kashe su? Falasɗinawa sun taru su na sumbatar fuskokin gawar yaran da ke cikin jini inda wasu ke zuba furannin ƙauna.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce su na aikin samar da tsagaita wuta a Gaza zuwa mako mai zuwa.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce ya ga ƙafar ƙwato kamammun Isra’ilawa da ke hannun Hamas a Gaza.

Netanyahu wanda ya aiyana cewa ƙasar sat a samu nasarar yaƙin da ta yi na tsawon kwana 12 da Iran, hakan a gare shi hanya ce ta buɗe ta ceto kamammun da Hamas ke garkuwa da su.

Tun 7 ga Oktobar 2023 Hamas ta kutsa yankin Isra’ila ta kama mutum 251 inda daga nan a ka shiga yaƙi ko kuma a ce Isra’ila ta yi ta kai miyagun hare-hare da jiragen yaƙi kan Gaza ta kasha fiye da Falasɗinawa dubu 50.

Hamas dai a yarjejeniya a baya ta sako wasu daga kamammun inda yanzu a ke tsammanin akwai saura mutum 50 ciki da 27 da Isra’ila ta ce sun mutu.

ƙungiyar masu bin diddigin ƙwato kamammun a Isra’ila ta nuna farin ciki cewa aƙalla yanzu Netanyahu zai maida hankali wajen karɓo waɗanda su ka saura a hannun Hamas.

Kazalika akwai gawar wani soja da Hamas ta ke ajiye da shi tun 2014 da ya mutu kuma shi ma Isra’ila na son a mika ma ta shi.

Amfani da ƙarfin soja kaɗai ba zai zama hanyar ceto mutanen da rai ba inda amfani da ƙofar yarjejeniyar tsagaita wuta ya zama mafi a’ala amma Isra’ila da ta kware wajen leƙen asiri da amfani da ƙarfin marar kima na iya aikata komai.

Wani sabon harin sojojin Isra’ila kan Gaza ya yi sanadiyyar kasha Falasɗinawa 17.

Kakakin rundunar kiyaye lafiyar farar hula na Gaza Mahmud Bassal ya baiyana cewa 16 daga wadanda a ka kasha ta sanadiyyar boma-bomai ne daga jiragen yaƙi a wajaje 5.

Bassal ya ce akwai yara biyu ma da a ka kasha a gidan su ta hanyar jefa mu su bom a Zeitun da ke Gaza kuma gaba ɗaya an daidaita gidan.

Isra’ila ba ta yi ƙarin haske nan take kan wannan kisan ba amma ta ce ta na dagewa ne don karya ƙarfin sojan mayakan Hamas.

Ma’aikatar lafiyar Gaza fitar da alƙaluman yawan mutanen da Isra’ila ta kasha zuwa yanzu a a yaƙin da sun kai 56, 412 kuma akasarin su mata ne da ƙananan yara. Majalisar ɗinkin Duniya na da kwarin gwiwa kan sahihancin alƙaluman.

KAMMALAWA

A iya tunani ba sai dai a zuba ido a ga yadda za ta kaya don ba yau a ka fara batun tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas ba kuma da zarar an samu dama sai wani abu ya ɓullo ta wani waje a sake komawa ruwa. Matuƙar Isra’ila na da ajandar lallai sai ta murƙushe Hamas kafin ta dasa waƙafi to ba alamun ranar daina zubar da jinin mata da ƙananan yara a Falasɗinu musamman Zirin Gaza.

By ukarofi