Tarihin tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Marigayi Manjo Janar Muhammadu Buhari, sojan Nijeriya mai ritaya, sannan kuma ɗan siyasa. Jajirtaccen mutum wanda ‘yan Nijeriya suke yi wa laƙabi da “Mai Gaskiya”. Wannan kalma ta ‘yan Nujeriya ta tabbata a kansa saboda kasantuwarsa marar hannu a cikin badaƙalolin maƙudan kuɗaɗen da mafiya yawa daga tsoffi da sabbin shugabannin Nijeriya suka tsunduma kawukansu a ciki.

Janar Muhammadu Buhari mutum ne da ke da gogayya a fannin mulki saboda aikin da ya yi a gidan soja, wanda ya fara tun daga sakan laftanar har sai da ya zamo shugaban ƙasa bayan tarin muƙaman da ya riƙe kafin hakan, sannan kuma bayan ritayar sa ya shiga siyasa wacce ta sake bashi damar sake ɗarewa kujerar shugabancin Nijeriya a karo na biyu kuma a matsayin farar hula.

Ya samu kafa tarihin cewa shi ne farkon ɗan Nijeriya da ya taɓa tsayawa takarar zaɓe a jama’iyyar hamayya sannan kuma ya kayar da shugaban da ke kan karagar mulki.

An haifi marigayi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan Disamban shekarar 1942 a ƙaramar hukumar Daura da ke jihar Katsina. Sunan mahaifinsa Adamu, mahaifiyarsa kuma Zulaihatu. Mahaifinsa ya rasu a lokacin da Janar Muhammadu Buhari ya ke da shekara huɗu kacal a duniya.

Ya fara karatu a matakin farko tsakanin Daura da Maiduguri cikin shekarun 1948 zuwa 1952, ya wuce Katsina Middle School a 1953, sannan ya halarci makarantar Sakandare proɓincial da ke Katsina a tsakanin 1956 zuwa 1961, anan ne ya samu takardar shaidar sakamakon jarrabawar kammala karatu ta Yammacin Afirka da a yanzu ake kira WAEC.

Daga nan ne Buhari ya shiga kwalejin horas da kananan hafsoshin soji a shekarar 1962.

A tsakanin shekarun 1962 zuwa 1963, marigayi Muhammadu Buhari ya je ƙarin horon aikin soji a kwalejin Mons Officer Cadet da ke Aldershot a Ingila.

Janar Olusegun Obasanjo ya zaɓe shi a matsayin kwamishinan tarayya na man fetur, inda a shekarar 1977, aka naɗa shi sakataren Majalisar ƙolin sojin ƙasar, kafin daga bisani ya riƙe muƙamin babban kwamandan sojoji na Kaduna.

Ya zama shugaban ƙasa ta hanyar juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Disamba 1983, amma aka hamɓarar da shi daga kujerarsa a wani juyin mulki da ya wakana a watan Agustan shekarar 1985.

Janar Muhammadu Buhari, ya riƙe muƙamai da dama tun fitowarsa ta farko daga makarantar soja da aka fara ƙaddamar da shi a matsayin sakan laftanar (second lieutenant). Manya daga cikin muƙaman da ya riƙe sun haɗa da: 

Gwamnan Jihar Arewa-maso-Yamman Nijeriya (Goɓernor North-Eastern Nigeria), a shekarar 1975, a zamanin mulkin shugaban Nijeriya Janar Murtala. 

Kwamishinan man fetur na tarayyar Nijeriya (Federal Commissioner for Petroleum Resources) muƙamin da ya ke daidai da na minister a yanzu, daga shekarar 1976 zuwa 1978. Ya riƙe wannan muƙami a zamanin mulkin soja na shugaba Janar Olushegun Obasanjo. 

Ciyaman na Kamfanin Manfetur na Nijeriya (Chairman, NNPC) a shekarar 1978. 

Shugaban rundunar sojojin Nijeriya ta uku da ke Jos (General Officer Commanding (GOC), Third Armored Diɓision of Jos) a shekarar 1983. 

Marigayi Buhari ya zama shugaban mulkin soja na tarayyar Nijeriya a shekarar 1984 har zuwa 1985 bayan an hamɓarar da gwamnatin farar hula ta shugaba Shehu Usman Shagari. 

Shugaban hukumar tara rarar manfetur (Chairman of Petroleum Trust Fund (PTF), daga 1995 zuwa 99 muƙamin da ya riƙe lokacin yana farar hula a zamanin mulkin shugaban soja na Nijeriya marigayi Janaral Muhammadu sani Abacha.

Shigarsa siyasa:

A shekarar 2003, Janaral Muhammadu Buhari ya shiga siyasa ƙarƙashin tutar jama’iyyar ANPP, jama’iyyar da ta bashi takarar shugaban kasa wanda ya shiga zaɓe tare da shugaba Janar Olushegun Obasanjo mai ritaya.

Muhammadu Buhari ya ƙara neman kujerar shugabancin Nijeriya a shekarar 2007, amma Umaru Yar’Adua ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya kayar da shi, inda ya sake tsayawa wata takarar a shekarar 2011 tare da tsohon shugaba Goodluck Jonathan, amma bai samu nasara ba.

Sai a 2015 ne ya samu nasara a babban zaɓen ƙasar ƙarƙashin jam’iyyar APC, yayin da ƙuri’un da aka kaɗa masa suka zarce na Jonathan da yawansu ya tasamma miliyan 2.5.

A ranar 29 ga watan Mayun 2015 aka rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa, kuma bayan ƙare wa’adi na farko, ya sake lashe babban zaɓen ƙasar a shekarar 2019, gabanin kammala mulkinsa a shekarar 2023.

A ranar Lahadi ne tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya koma ga mahaliccinsa yana da shekaru 82 a duniya, a wani asibiti da ke birnin Landan, bayan fama da rashin lafiya. 

Tsohon shugaban ya mulki Nijeriya tsakanin 1983 zuwa 1985 a mulkin soja gabanin zaɓen shi a matsayin shugaban ƙasa na mulkin farar hula ƙarƙashin demokraɗiyya daga shekarar 2015 zuwa 2023. Tun gabanin zaɓenshi a matsayin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya riƙe manyan makamai a matakai daban-daban. 

By ukarofi