Ki girmama ƙa’idodin doka – Majalisar Dattawa ga Natasha

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dattawa ta gargaɗi Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan kan cewa ta ƙaurace wa halartar zaman da ta saba yi a zauren majalisa, inda ta ce ba ta amince da ta dawo aiki a yanzu ba.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na majalisar, Sanata Yemi Adaramodu ya yi gargaɗin a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi.

Da fari, Sanata ta ci alwashin koma wa aikinta a majalisar a ranar Talata, 22 ga Yuli, bayan ta aika wa majalisar sakon shirinta na koma wa a ranar.

Saidai, Adaramodu ya ce babu wani sahihin umarni daga kotu da ya ba ta damar komawa majalisar nan da nan, yana mai cewa akwai sharuɗɗa da aka samar, waɗanda wajibi ne tq bi su gabannin ta koma zuwa aiki.

Don haka ne ta gargaɗi Natashar da ta nesanta kanta daga harkokin majalisar har zuwa lokacin da za a ba ta damar komawa a lokacin da ya dace.

By Babaji